Dr.
Sulaiman Muhammad Adam (An haife shi ranar 14 ga watan Yuni shekarar 1962), babban limamin Masallacin Sultan Bello dake unguwan sarki Kaduna a halin yanzu. Dakta Sulaiman Muhammad Adam ya fara jagorantar Sallar Juma’a a Masallacin Sultan Bello a ranar 6 ga watan Janairu shekara ta 2017.
Suleiman Muhammad Adam | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 14 ga Yuni, 1962 (61 shekaru) |
Sana'a |
Sulaiman yayi karatun firamare a ƙauyen Umoko a Jihar Ribas, kudancin Najeriya. Bayan kammala karatun firamare sai ya zarce zuwa sakandare inda yayi Higher Islamic Studies (H I S) a Jos, a lokacin kuma ya shiga kwalejin Arabic Teachers College Grade 3. Daga nan kuma ya cigaba da karatunsa a kwalejin ilimi ta Kano, inda ya samu shaidar gama karatun NCE. Ya kuma samu shaidar digiri a Madina da kuma Maleshiya, inda ya karanta Larabci, Shari'a da kuma Ilimin Addinin Musulunci. Haka kuma tsohon Lakcara ne a Jami'ar Jihar Kaduna.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Suleiman Muhammad Adam, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.