(Poliomyelitis) a harshen Turanci wato Cutar Polio ko kuma Cutar shan inna cuta ne da ake iya dauka daga wani ta dalilin kwayoyin cutar polio (poliovirus).
Kusan kaso 75% na cutar basa nuna alamomin cutar; ana iya samun kananan alamomi kamar ciwon makoshi da zazzabi; a yawancin lokuta alamomi kan tsananta kamar ciwon kai, ciwon wuya, da kuma Paresthesia. Wadannan alamomi sukan wuce a tsakanin mako daya ko biyu. Alamar gama-gari itace shanyewar sashin jiki na dundundun, da kuma mutuwa a wasu lokuta idan tayi tsanani. Ana iya samun alamomin cutar (post-polio syndrome) shekaru kadan bayan warke daga cutar, da kuma habakar karancin karfi gabbai irin wanda mutum ke fuskanta yayin kamuwa cutan.
Polio | |
---|---|
Description (en) | |
Iri | viral infectious disease (en) , peripheral neuropathy (en) , acquired motor neuron disease (en) , central nervous system viral disease (en) , Enterovirus infectious disease (en) cuta |
Specialty (en) | infectious diseases (en) , neurology (en) orthopedics (en) |
Sanadi | poliovirus (en) |
Symptoms and signs (en) | muscle weakness (en) , paralysis (en) , paresis (en) , meningism signs (en) , zazzaɓi, amai gudawa |
Effect (en) | Otter Valley polio epidemic (en) 1916 polio epidemic (en) |
Disease transmission process (en) | fecal–oral route (en) contact transmission (en) |
Physical examination (en) | physical examination (en) , viral culture (en) Q25438941 |
Suna saboda | Jakob Heine (en) da Karl Oskar Medin (en) |
Identifier (en) | |
ICD-10-CM | A80.9, A80, A80.3, A80.2, A80.4, A80.1 da A80.0 |
ICD-9-CM | 045, 045.9, 045.92 da 045.90 |
DiseasesDB | 10209 |
MedlinePlus | 001402 |
eMedicine | 001402 |
MeSH | D011051 |
Disease Ontology ID | DOID:4953 |
Cutar shan inna na faruwa ne hakanan ne ga dan-Adam. Tana da saurin yaduwa matuka, kuma tana yaduwa daga wani zuwa wani ta hanyar cudanya ta baki ko fuska (misali a dalilin gurbataccen muhalli, ko kuma ta hanyar cin abinci ko shan ruwa da ke dauke da kashin dan-adam), ko kuma ta hanyar cudanya ta baki da baki. Wadanda suka kamu da cutar suna iya yadata ga sauran mutane har tsawon makonni shida ko da ace basu fara nuna wasu alamomi ba. Ana iya gano asalin cutar ta hanyar nemo kwayar cutar a cikin kashin mutum ko kuma nemo kwayoyin halitta masu fada da kwayoyin cuta acikin jini.
Poliomyelitis (kwayoyin cutar shan inna) sun wanzu na tsawon shekaru dubunnai da suka gabata, tare da nuna cutar acikin zanukan zamunan baya. Wanda ya fara gano wannan cutar wani masanin magunguna ne bature dan Ingila Michael Underwood a matsayin cuta mai rudarwa acikin shakarar 1789, sannan kuma an fara gano kwayoyin cutar da ke janyo cutar a shekarar 1909, wanda wani mai binciken kwayoyin kariyar jiki dan kasar Austriya Karl Landsteiner. An samu manyan barkewar cutar acikin karni na 19 a kasashen Turai da Amurka, sannan acikin karni na 20, cutar ta zamonta cuta mafi tada hankali acikin cututtukan da ke kama kananan yara. Bayan gano rigakafin cutar acikin shekarun 1950s, cutar shan inna ta ragu acikin sauri.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Polio, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.