Akure

Akure birni ne, da ke a jihar Ondo, a ƙasar Nijeriya, kuma itace birni mafi girma kuma babban birnin jihar Ondo.

Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2006. akwai jimilar mutane 484,798 (dubu dari huɗu da tamanin da huɗu da dari bakwai da casa'in da takwas). An gina birnin Akure a karni na sha biyu.

AkureAkure
Akure

Wuri
Akure
 7°15′00″N 5°11′42″E / 7.25°N 5.195°E / 7.25; 5.195
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaOndo
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 847,903 (2010)
• Yawan mutane 855.6 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 991 km²
Altitude (en) Fassara 350 m
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1150
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 340106
Kasancewa a yanki na lokaci
Tsarin lamba ta kiran tarho 234
Akure
Akure.
Gajeren zance na tarihin Akure cikin yaren Akure daga ɗan asali harshen

Tarihi

Kafin 1914

An samu ragowar tsofaffin dutsu tun na zamanukan da suka gabata a wajen birnin Akure. Har wayau an samu ragowar kasusuwar mutanen da, wanda su ne ragowar mutanen da mafi tsufa da aka taba samu a Afurka ta kudu kimanin shekaru 11000 sukayi rayuwa a baya da suka wuce.

Tarihin gargajiya na tatsuniyoyi sun nuna cewa birnin Akure ta samo asaline daga Omoremilekun Omoluabi, tattaba-kunnen sarki Oduduwa. Yarima Omoluabi ya bar Ile-Ife, masarautar kakanshi ne domin neman wurin zama bayan yaci wata tsatstsaurar gwaji da sarkin Yarbawa na lokacin yayi masa da kanshi, a yayinda ya iske birnin a yankin Akure na yanzu. Fadar sarki (Oba) na a tsakiyar birnin, wacce aka gina a shekara ta 1150 AD. Fadar na da harabobi 15, kuma kowacce nada amfaninta. Misali, a harabar Ua ubura ake rantsuwa da alkawari, a harabar Ua Ikomo ake radin suna, Wasu daga cikin sunayen harabobin sun hada da Ua nla, Ua Ibura, Ua jemifohun, Ua Ikomo. Yanzu an gina wani sabon fada na kirar zamani a yankin kudancin tsohuwar fadar. Oja Oba watau kasuwar sarki tana nan kusa da fadar.

Ana kiran sarkin Akure da "Deji of Akure", wanda hakimai shida ke tayashi gudanar da harkokin sarauta. Gunkin Akure shine mahaifin Omoremilekun Omoluabi wanda ake kira da "Ekun" ma'ana damisa (shine inkiyarsa na sarauta). Wannan dalilin yasa duk wani dan Asalin Akure ake masa lakabi da "Omo Ekun"

Daga 1914 zuwa yanzu

A shekarar 1915, gwamnatin turawan mulkin mallaka suka hade yankunan Owo, Ondo da Ekiti wacce ta samar da sabuwar gunduma da cibiyar ta a Akure. Birnin Akure ta zama babban birnin Onda a shekara ta alif 1976.

An nada Adebiyi Adegboye Adesida Afunbiowo II, a matsayin sarkin Akure a ranar 13 ga watan Augusta, shekarar 2010, don gadon kujerar Oba Oluwadamilare Adeshina wanda aka tsige a ranar 10 ga watan June, shekarar 2010, a dalilin rashin da'a ga ababe masu tsarki da daraja. Daga bisani an nada diyar tsohon sarki Afunbiowo, Omoba Adetutu matsayin sarauniya a ranar 30 ga watan Nuwamba, shekarar 2013, bayan tsigeshi.

A shekara ta 2015, An nada Omoba Kola Aladetoyinbo matsayin sarki, bayan ya buge yan takara 12 wanda gidan sarauta na Osupa suka gabatar don zama sarkin Akure na 47.

Labarin Kasa

Birnin Akure na nan a 7°25’ daga arewacin equator, da kuma 5°19’ daga kudancin Meridian. Tana da nisan kimanin kilomita 700km (430 mi) daga kudu-maso-yammacin Abuja, da kuma kilomita 311km (193 mi) daga arewacin Lagos. Akwai bambancin yawan mutane dangane da wuraren zama, wasu daga ciki misali Arakale, Ayedun Quarters, Ijoka, da kuma Oja-Oba suna da kimanin mutum 200 a kowacce hekta guda. A yayinda wasu yankunan kuma kamar Ijapo Estate, Alagbaka Estate, Avenue da kuma Idofin suke da kimanin mutum 60 zuwa 100 a kowacce hekta (24 and 40/acre). Birnin ya fada cikin kasafin yanayi na tropic rainforest zone na Najeriya.

Tattalin arziki

Akure na da gidajen telebijin guda biyu da kuma gidajen rediyo guda takwas: wanda suka hada da NTA Akure, Ondo State Television, Sunshine Radio Akure, Adaba FM, Futa FM, Empire Radio, Positive FM Akure, Orange FM, Galaxy Radio, Crest FM, and Breeze FM.

Akure itace cibiyar kasuwanci na yankunan da ake noma kamar na cocoa, doya, rogo, masara, taba da dai sauransu. Har wayau ana noman auduga kuma ana amfani dashi wajen samar da kayan sanyawa a yankin. Hatsi da aka fi nomawa a yankin sun hada da; shinkafa, wake da dawa.

Wuraren kaswanci

Akwai wuraren cin abinci da ya a birnin Akure kamar Chicken Republic, Tantalizers, Captain Cook, Mr. Bigg's, LAH Kitchen & Lounge da dai sauransu. Manyan shaguna kuma sun hada da; NAO supermarket, AFOYEM supermarket, CECI supermarket, PEP stores, Omega supermarket, and DE CHRIS supermarket, OUK supermarket, God's Love supermarket da dai sauransu. Akwai kuma Shoprite Akure mall.

Harkokin Lafiya da Ilimi

A asbitocin birnin Akure akwai kwararrun ma'akatan kiwaon lafiya wanda aka horar sosai don kare lafiya al'umman garin. Har wayau akwai karin wuraren shan magani na gwamnati da kuma wuraren da ba na gwamnati ba. Shirin 'Abiye' health programme wanda Gwamnatin Oluseegun mimiko suka gudanar akan kula mata masu haihuwa da shayarwa ya samu karbuwa a wajen WHO wanda yana daya daga cikin mafi kyawun shirin lafiya da aka taba gudanarwa tare da samar da asibitin Mother-Child hospital.

Birnin na dauke da jami'oi wanda suka hada da; Federal University of Technology Akure, Federal College of Agriculture, School of Nursing and Midwifery, and School of Health Technology. Har wayau tana da sanannun makarantun sakandare da suka hada da; St. Thomas Aquinas College, Oyemekun Grammar School, St. Louis Grammar School, and Fiwasaye Girls' Grammar School. Har wayau birnin na dauke da makarantun gwamatin tarayya wanda suka hada da Girls' College da St. Peter's Unity Secondary School da dai sauransu.

Birnin Akure

A karkashin masarautar Akure na yanzu akwai kananan masarautu guda biyu wanda suke da nasu sarakunan. Birnin ta kasancewa mahaifa ga wasu manyan mutanen Najeriya kamar Chief Olu Falae, Dr Akinola Aguda da sauran sanannun mutane a fannin boko, soji, shari'a da sauran fannukan gwamnati. Philip Emeagwali, wanda ya lashe gasan Gordon Bell Prize, mahaifiyar Sunny Adé, Ralph Alabi (tsohon chairman na kamfanin Guniness Nigerian Ltd), da kuma Kole Omotosho duka yan asalin Akure ne.

Wasanni

A fannin wasanni, Akure da katafaren filin wasan kwallon kafa da ke iya daukan mutum kimanin 15,000. Akwai wani sabon filin da ake ginawa daga kudanci birnin.

Addinai

Akure birni ne dake dauke da mutane mabiya addinai iri-iri; kamar kiristoci, musulmai da kuma masu bin addinin gargaji ko kuma bautan gumaka. Akwai cocuka da dama a garin, akwai babban masallaci (Central Mosque) bisa hanyar Oba Adesida Road wanda yana daya daga cikin kayatattun wurare a garin. Abun jinjinawa shine mutanen Akure na zama lafiya da junansu.

Siyasa

Akure tana da dan majalisa dake wakiltan ta a majlisar dokoki watau Hon. Simeon Toluwani Borokini (Akure South I), Hon. (Dr.) Abiodun Faleye (Akure North) da kuma Hon. Olajide David Sunday (Akure South II).

Sanannun Mutane

Hotuna

Manazarta

Tags:

Akure TarihiAkure Labarin KasaAkure Tattalin arzikiAkure Harkokin Lafiya da IlimiAkure Birnin Akure WasanniAkure AddinaiAkure SiyasaAkure Sanannun MutaneAkure HotunaAkure ManazartaAkureNijeriyaOndo (jiha)

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Shehu Musa Yar'AduaKasashen tsakiyar Asiya lAdam A ZangoNew DelhiGeronay WhitebooiFiqhun Gadon MusulunciLefeYobeBuka Suka DimkaItofiyaRabi'a ta BasraSumayyah yar KhabbatZamfaraAsibitin MurtalaAmurka ta ArewaJerin kasashenKafin HausaAfirka ta KuduJodanUnelle SnymanMikiyaBirtaniya Yammacin AfirkaAhmad Ali nuhuEdith MolikoeMahmoud AhmadinejadRwandaShugaban NijeriyaNew OrleansFinlandRundunonin Sojin NajeriyaAbdul Samad RabiuJerin gidajen rediyo a NajeriyaKogin HadejiaHadiza Bala UsmanIraƙiHauwa SuntaiMaryam Bukar HassanƘuli-ƙuliIbrahim Ahmad MaqariPrincess Aisha MufeedahMusulunci AlkahiraMagaryaNew York (birni)Gombe (jiha)DamaturuCNNSaudi ArebiyaHenriette MollerAbubuwan Al'ajabi Bakwai na Tsohuwar DuniyaYaren TyapYakubu GowonSani SabuluMain PageSankaran NonoSautiNasarawaWikisourceBahati BukukuArise PointMasallacin tarayyar NajeriyaYaƙin Duniya na IJegoAdo BayeroLibyaRubutaccen adabiLittafiBornoJinin HaidaFatima Ibrahim ShemaSudanTambarin NajeriyaAminu AlaDele AlliSo🡆 More