Paris Saint-Germain Football Club, , Anfi sanin su da Paris Saint-Germain, Paris SG, ko PSG,ta kasan, ce kulub din kwararrun kwallon kafa ce dake a birnin Paris na kasar Faransa.
An kuma kafa kulub din a shekarar 1970, kulub ta kasan ce tana sa kaya masu launin ja da shudi, ne.PSG na buga wasan gida a filin ta mai daukan adadin mutane, 47,929 wato Parc des Princes dake 16th arrondissement na Paris tun daga shekarar 1974. Kulub din na buga The club plays in the babban rukuni na kwallon kafar faransa, Lig 1.
Paris Saint-Germain | |
---|---|
Bayanai | |
Suna a hukumance | Paris Saint-Germain Football Club |
Iri | ƙungiyar ƙwallon ƙafa |
Masana'anta | Q112166181 |
Ƙasa | Faransa |
Mulki | |
Shugaba | Nasser Al-Khelaifi (en) |
Hedkwata | Faris |
Subdivisions | |
Tsari a hukumance | Société anonyme sportive professionnelle (en) da public limited company with a board of directors (n.o.s.) (en) |
Mamallaki | Qatar Sports Investments (en) |
Sponsor (en) | Accor (en) |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 12 ga Augusta, 1970 |
Wanda ya samar | Guy Crescent (en) |
Wanda yake bi | Stade Saint-Germain (en) |
|
Paris, Saint-Germain ta mayar da kanta babbar Kulub a Faransa, kuma daya daga cikin manyan kulub a cikin gasar kwallon kafa a Turai na wannan lokaci. PSG, ta lashe adadin kyautuka guda 38, haka yasa ta zama Kulub din data fi samun nasara a kasar faransa da adadin yawan data samu. PSG kuma ita kadai ne Kulub a Lig 1 wanda bata taba zuwa riligeshan ba, kuma kulub din data fi kowace Kulub adadin yawan kakannin wasa ajere a babban mataki tayi wasa a kaka 45 na Lig 1 tun daga shekara ta 1974), tana daya daga cikin kulub din Faransa biyu da suka taba lashe Manyan gasar Turai, kuma kulub mafi shahara a Faransa, tana daga cikin kulub din dake da yawan mabiya a duniya.
A gida (Faransa), PSG ta lashe gasar Lig 1 guda bakwai, da tarihin lashe guda goma sha biyu Coupe de France, da tarihin lashe Coupe de la Ligue guda takwas, da tarihin da wasu na lashe Trophée des Champions guda takwas. PSG kuma ta lashe Lig 2 daya. A kwallon kafar nahiyar Turai, ta lashe UEFA Cup Winners' Cup daya da kuma UEFA Intertoto Cup shima daya. PSG nada dogon hamayya da Olympique de Marseille. Wanda wasa tsakaninsu shine babban gasar dake da kalubale, ana masa lakabi da Le Classique.
Qatar Sports Investments (QSi) sune masu kulubin din tun daga shekarar 2011 (a wancan lokaci sunan su Qatar Investment Authority). Suna mallakar kulubin din, sai Paris SG tazama mafi tsadar kulubi a Faransa kuma daya daga cikin mafi tsada a duniya. PSG itace na bakwai cikin kulubi masu yawan kudin shiga a duniya da adadin kudin da suke samu a shekara da ya kai €486.2m, kuma sune na 11 cikin kulubi masu tsada a duniya, da Kumar kudin da ya kai €825m. A watan February a shekara ta 2019, Kwallon Kafar Faransa suka sanya Paris SG amatsayin na bakwai cikin manyan kulubin dake duniya..
.
.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Paris Saint-Germain, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.