Keffi karamar hukuma ne, da ke a jihar Nasarawa, a ƙasar Najeriya .
Hedkwatar ta tana cikin garin Keffi. Keffi na da tazarar kilomita 50 daga Abuja. Jami'ar Jihar Nasarawa tana garin Keffi zaune a kan hanyar Keffi zuwa Akwanga.
Keffi | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jiha | Nasarawa | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 138 km² | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Yana da yanki 138 km2 da yawan jama'a kusan 2 a ƙidayar ta shekara ta 2006. Lambar gidan waya na yankin ita ce 961.
An kafa garin Keffi a shekara ta 1802 a hannun wani jagoran Fulani Abdu Zanga wanda ya karbi sarautar sarki. Karamin mulkinsa ya kasance karkashin masarautar Zariya wanda sai da ta rika biyan harajin bayi a duk shekara.
A cikin shekarar alif ta 1902 Keffi ne wani lamari ya faru wanda ya kai ga mamaye Arewacin Najeriya, bayan “magaji”, wakilin Sarkin Zariya ya kashe wani Bature. A lokacin da Magaji ya samu mafaka a Kano, wannan shi ne dalilin da Lugard ya sanya ya mamaye halifancin arewa.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Keffi, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.