Kyauta A Mahangar Addinin Musulunci.

Al’amarin kyauta a mahangar addinin Musulunci, ana iya cewa baiwa ce, kuma ibada ce  muhimmiya.

Kyauta A Mahangar Addinin Musulunci.

Al’amarin kyauta a mahangar addinin Musulunci, ana iya cewa baiwa ce, kuma ibada ce  muhimmiya.

Bisa dalilin muhimmancinta yasa Allah (S.W.T) Ya yi ummarni da yin kyauta.  A  daya bangaren, sai aka kwadaitar da yawaita kyauta tare da bayyana fa’idojin da kyauta ke jawowa wanda ya yi ta. Akwai ayoyi da yawa wadanda aka tsoratar da yin rowa, tare da nuna illolin da take jawo ma mai yinta, watau marowaci.

Bayan ayoyin qur’ani kuma,  akwai hadisai masu yawa da suka nuna muhimmancin kyauta. A musulunci an kira kyauta (bayarwa) da sunaye daban daban kamar: zakka da zakkatul fitir (zakkar kono) da  imfaƙi(ciyarwa) da wakaf (bayar da gida ko gona ko makaranta) da wasiyya da layya da hadaya da sauransu.

Kyauta Da Sadaka

Kyauta da Sadaka suna da kusanci da juna matuƙa don sun yi kama, sau da yawa abin dakan bambanta su ita ce niyya.

Manzon Allah (SAW) yana kar:ar kyauta, amma ba ya karbar sadaka. Bukhari 3.751.

Manzon Allah (saw) ya tabbatar cewa kar a bai wa iyalan gidan Muhammad sadaka. Muslim ya riwaito.

Abu Huraira ya ce: wata rana Hassan ya dauki kwayar dabino. Manzon Allah  ya ce kai fito da shi ba ka san mu ba ma cin sadaka ba? Fiƙhus sunna 3.73B  

An taba bai wa Barira sadakar nama, amma ta kawo wa Annabi (SAW), sai Annabi ya ce: ke sadaka a gareki mu kuma ya zama kyauta. Bukhari 2.571.

Daga Abu Huraira ya ce: "Idan aka kawo abinci zuwa ga Manzo Allah(SAW), yakan tambaya cewa kyauta ko sadaka? Idan aka ce sadaka ce, sai ya ce Sahabbai su ci, amma in aka ce kyauta ce, sai ya ci tare da Sahabbai. 3.750.

Zakkah: Sadaka (kyauta) ce ta wajibi watau ita farilla ce, amma ga mai wadata.

Sadakatul Jariya: Manzon Allah (SAW) ya ce: Idan mutum ya mutu dukkan ayyukansa sun yanke.  In ban da ayyuka uku, sadaka mai gudana da ilmin da ya koyar ake aiki da shi, sai kuma natsattsen Ɗa wanda zai rinka yi masa addu’a. Fiƙhus Sunna 104 A.   

Daga Anas Bin Malik ya ce: Duk wanda ya dasa bishiya ko ya shuka dan itace ya tsira ya yi Yaya , wani tsuntsu ko dabba ko mutum ya ci daga gareta. Wannan kamar sadaka ce mai gudana.Bukhari 3.513

Shari’ar  Musulunci ta shardanta wasu hukunce-hukunce don ladabtarwa, a inda ta yanke cewar a ciyar da abinci (kyauta) ko a yanta baiwa. Kamar wajen kaffarar azumin watan ramalana, inda aka ce duk wanda ya karya azumi da gangar, sai ya yi azumi sittin, ko ya yanta baiwa, ko ya ciyar da mutane sittin. Wannan ciyarwa alama ce ta kyauta wadda yake kishiyar rowa ce, don haka Musulunci ba ya son Musulmi ya zama marowaci.

Bayan wannan kuma sai kaffarar rantsuwa, nan ma ko dai mutum ya yi azumin kwana uku, ko ya ciyar da mutane goma abincin da zasu  koshi.

Bayan wannan tsari kuma, sai bangaren da aka umarci Musulmai da su yi kyauta, su ba da zakka da sadaka da wakafi. Dukkan wadannan suna korar ko kawar da rowa a tsakanin Musulmai.

Sada Zumunci Da Kyauta

Ana iya sada zumunci ta hanyar yin  kyauta, zumuncin zai iya kasancewa naka ko na waninka. Bayan haka kuma zai iya faruwa a tsakanin mutane rayayyu (masu rai) da matattu (wadanda suka rasu). Haka iyaye ko mata ko yayye da sauransu.

“Manzon Allah  (Sallallahu Alaihi Wasallam). Ya kasance ya rinka bayar da kyauta zuwa ga kawaye Khadija matarsa ta farko ko bayan da ta rasu. A’isha (R.A.) ta riwaito cewa: “Ban taba jin kishin wata mata daga cikin matan Manzon Allah ba, kamar yadda nake kishin Khadija, duk da yake ban taɓa ganinta ba.

Manzon Allah yakan yawan tuna ta tare da ambatonta, kuma in ya yanka rago yakan Debi naman ya bayar ya ce a kai wa wasu daga kawaye Khadija.  Wata rana na taba ce masa ka damu da Khadija matuka, tamkar ba wata mace a Fadi duniyar nan sai  Khadija. Yace: “ Khadija  ta yi min  komai a rayuwa wanda ba wani da ya yi min kamar haka, sannan  daga gareta na samu Yaya ”.   Bukhari 5.166.

Akwai wani bayani wanda ya faru a zamanin Sahabbai, inda Abdullahi Ibn Umar zai tafi  aikin hajji. Suna cikin tafiya da jama’arsa, sai suka hadu da wani Balaraben kauye. Abdullahi Ibn Umar  nan da nan, sai ya dauki abin hawansa da jabba ya ba shi, sannan kuma ya girmamashi. Bayan sun rabu sai aka tambayi Ibn Umar game da wannan mutumin, sai Ibn Umar yace:

"Mahaifin mutumin abokin Sayyidina Umar Bin Khaddaf ne”. Ibn Umar ya Kara da cewa: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “ku sadar da zumuncin da iyayenku suke yi suna raye ko bayan sun rasu”.

Kyauta Ga Makwabta:

A’isha ta ce: “Ya Manzon Allah, ina da makwabta biyu wane zan bai wa kyauta daga cikinsu? Manzon Allah ya ce: “ki bai wa wanda kofarsa ta fi kusa da ke. Bukhari. 3.767   

A’isha (R.A.) ta riwaito cewa: Manzon Allah yana yanka akuya ya rarrabar da naman, sai ya tambaya ko akwai abin da ya rage?A’isha ta ce saura karfata, sai Annabi ya ce nama na nan, karfata ce aka rasa.Tirmizi ya riwaito.

Ladubban Kyauta a Musulunci:

Kyauta na da wasu ladubba wadanda shari’a ta tsara don al’umma su kiyaye.  Akwai na umarni da kuma na hani da na kwadaitarwa da na tsoratarwa da sauransu.

Abubuwa Da Suke bata Kyauta Ko Sadaka

Akwai wasu abubuwa wadanda mutum zai yi su bata masa kyauta ko sadakar da ya yi. Da farko akwai riya ko gori ko zobe ko tasau da sauransu.

Riya

Na nufin ka yi wa mutum kyauta ko sadaka ba wanda ya sani, ka zo kana bayar da labari don a yaba maka. Tabbas riya  na bata aiki komai yawansa.

Gori

Na nufin ka yi wa mutum kyauta ko sadaka, amma daga baya ka rinka cewa, ashe  ba na yi maka kaza da kaza ba?  Hakika gori na bata kyauta ko sadaka saboda tana tozarta wanda aka yi wa.  Wannan  ya sa Manzon Allah ya hana, Allah (swt) Ya hana a cikin Alqur’ani a inda Yace: “kar ku bata sadakar ku da gori da zobe”

Zobe

Na nufin ka yi wa mutum kyauta ko sadaka, amma daga baya ka kwace abin da ka bayar.  Wannan shi  ma shari’a ta hana, saboda ta haifar kiyayya a tsakanin wanda aka yi wa kyauta ko sadaka da wanda ya yi.  

Bisa kyakkyawar  dabi’a duk wanda ya aikata wannan ana daukarsa karamin mutum. Bisa shari’a kuwa, shi ma wannan abin kyama ne. Akwai wani hadisi mai yin haka ya yi kama da kare. Domin kare ya ke yin amai sannan daga baya yana dawo ya lashe abisa.

Tasau

Na nufin mutum ya yi wa budurwa ko bazawara toshi (kyauta).  Bayan ya yi  mata toshi  sai daga baya ya tayar  da kyautar wato ya kwace. Bisa kyakkyawar  dabi’a duk wanda ya aikata wannan ana daukarsa karamin mutum ma’ana mai karanta. Duk wanda aka san shi wannan hali ba ya yin farin jini a gari. Bugu da kari Yanmata kan guje shi.

Raina Kyauta

A al’adance an hana mutum ya raina kyautar da aka yi masa, saboda Bahaushe ya ce: “maraina  kaɗan ɓarawo ne”, ko “lomar hasafi ta fi kaɓakin tsiya” ko “da babu gara ba daɗi”.

Haka kuma ko a musulunce shari’a ta hana raina kyauta kamar a wani hadisi inda Abu huraira ya ce:Manzon Allah ya ce: “ya ku mata kar ɗaya daga cikin ku ta raina kyautar da ƙawarta ko maƙwabciyarta ko da kofatan akuya ne”.Bukhari 3.740

Daga  Abu huraira ya ce: Manzon Allah Ya ce: zan amsa gayyata walima ko da abincin kofaton akuya ne.

KYAUTAR DA MUSULUNCI KE KYAMA.

Abdullahi bn Umar da Abdullahi Abbas sun ruwaito cewa: Manzon Allah (SAW) haramun ne mutum ya bayar da kyauta ko sadaka, sannan daga baya ya zo ya ƙwace, sai tsakanin uba in yaba ɗansa. Duk wanda yayi kyauta ya koma mata ya zama kare mai yin amai ya dawo lashe. Abu Dauda 1571.

Abu umama ya ruwaito cewa: Manzon Allah yace "duk wanda ya taimaki ɗan uwansa sannan ya karɓI wata kyauta daga gare shi to tinkari wata ƙofa daga ƙofofi riba (rashawa). 1573

Abdullahi bn Ammar bn As ya ce: Manzon Allah ya ce: ba a yarda ba mace ta yi kyauta da wani abu daga kayan mijinta ba, sai da izininsa.  Abu Dauda 1575.

Nu’uman bn Bashir yace: Babansa ya tafi da shi wajen Manzon Allah, ya ce: Na baiwa Ɗana bawa, sai Manzon Allah ya tambaya ka bai wa sauran Ƴaƴanbka kamar haka?  Sai ya ce: a’a, Manzon Allah ya ce: karɓi kyautarka. Bukhari3.759.

       

A  ƙarshe,  ga  wasu ƙarin hujjoji kaɗan don a sanya su a matsayin madogara. Waɗannan hujjoji sun ƙunshi ayoyin Ƙur’ani da wasu hadisai, da kuma maganganun wasu bayin Allah.

Gaba Ɗayansu sun yi nuni ne ga fa’idar bayarwa  (kyauta ko sadaka ko zakka)  a Musulunce da kuma cewa bayarwa ibada ce ga mahangar Musulunci. Bayan haka kuma baiwa ce domin kuwa sai wanda Allah Ya yarda da shi yake yin alheri.

An ambaci sadaka Suratul Baƙara aya ta 219, 270, 272, 274, 291,  Ala’imrana aya ta 92,  134,  Nisa’I aya ta 114,  Tauba aya ta 60, 79, 103,  Nur  aya ta 56, Mujadala aya ta 12, 13,

An yi ummarnin yin sadaka a Suratul Baƙara aya ta 271,

An ambaci fa’idoji da falalar sadaka Suratul Baƙara aya ta 261, Anfal aya ta 60, Suratul Hadid aya ta18, Tagabun aya ta17.

An tsoratar a kan ƙin yin sadaka Suratul Suratul Isra’il aya ta 28, ayoyi da  surori masu yawa a Ƙur’ani mai girma :

Suratul Isra’il aya ta 29. Kar ka maƙe hannunka ka zama marowaci, kar kuma ka zama almubazzari don kar ka zama abin zargi, ko ka talauce.

A cikin Suratul Laili. Da Suratul Ma’uun, da cikin Suratul Hadid.

Abu Huraira ya ruwaito Annabi ya ce:  “mai kyauta yana kusa da Allah, kuma kusa da Aljannah, kuma kusa da mutane. Amma marowaci kuwa yana nesa da Allah, kuma yana kusa da wuta. Jahili wanda yake yin kyauta ya fi kusa da Allah fiye da mai ibada marowaci. Tirmizi: 580:

Aliyu Ɗan Abi Ɗalib yace: Malami saboda iliminsa yana iya zama mai kyauta. A inda mai dukiya saboda son dukiyarsa yana iya zama marowaci.

A Musulunci, an fifita mai bayar da kyauta a kan wanda yake karɓa. kamar wani hadisi dayace: Hannun sama (Mai bayarwa) yafi hannun ƙasa (mai kar~a) daraja. Duk wannan ana nuna kyawun kyauta fiye da rowa da kuma kwaɗayi.

Ibn Abbas ya ce, Manzon Allah shi ne mafi alheri (Kyauta) a mutane. Ya fi yin kyauta a watan azumi, ya fi iska kyauta.1.1

Abdullahi Bin Amr ya ce, wani mutum ya tambayi Annabi cewa: Wane aiki ne ya fi a musulunci? Sai ya ce ka ciyar da talaka, sannan ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba. Bukhari 1.11.

Tattaunawa

Tags:

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Hassan Usman KatsinaYakin HunaynIbrahim NiassAbdullahi Bala LauCiwon sanyiMuhajirunArewacin NajeriyaAmina Sule LamidoSiriyaSallar Matafiyi (Qasaru)MkpaniMansura IsahKamaruBeninRikicin makiyaya da manoma a NajeriyaEnioluwa AdeoluwaAbzinawaNicki MinajNamijiBuka Suka DimkaDauda LawalNairaImam Malik Ibn AnasRashaUmm HabibaOsheniyaJerin ƙauyuka a jihar YobeAbubakar Atiku BaguduMatan AnnabiMuhammadu MaccidoTaliyaRundunonin Sojin NajeriyaGiadeRumawaTarihin Jamhuriyar NijarMasarautar BauchiAliko DangoteKulawar haihuwaNorwayLagos (birni)Falalar Azumi Da HukuncinsaAbdullahi AdamuAbubakar WaziriAminu KanoHamisu BreakerKaduna (jiha)Sawda bint Zam'aSarauniya MangouSatoshi NakamotoZainab Ujudud ShariffHarshe (gaɓa)Johnson Bamidele OlawumiSunayen Annabi MuhammadHarshen HausaGaurakaIbrahim Ahmad MaqariMasarautar DauraMuhammadu Sanusi IRahama SadauTabarmaAngel HsuAbujaTaj-ul-MasajidYusuf (surah)DJ ABKomorosSinMbieriRubutaccen adabiZakiUmaru Musa Yar'AduaAustriyaMuhammad Yusuf🡆 More