Muhammad Yusuf

Muhammad Yusuf Ya kasance kuma an Haife shi a ranar: 29 ga watan Janairun Shekara ta 1970 - ya Mutu a ranar: 30 ga watan Yulin shekara ta 2009), kuma an san shi da Ustaz Mohammad Yusuf, dan Nijeriya ne kuma malamin addinin musulunci ne.

Muhammad Yusuf
Muhammad Yusuf Mukala mai kyau

wanda ya kafa akidar cewa karatun boko haramun ne, an masa kallan dan ta'adda wanda ya kafa kungiyar Boko Haram a Najeriya a shekara ta 2002, wanda yanzu haka tasirin wannan gungiyar ta Boko Haram ya shiga kasar Nijar, Cadi, da Kamaru, Shi ne shugaban ta na farko har aka kashe shi a rikicin Boko Haram na farko a cikin garin Maiduguri , wanda daga baya mataimakin sa Abubakar Shekau ya ci gaba da jagoranta. Muhammad yusuf ya kasance yana bibiyan karatun Mallam Ja'afar Mahmud Adam wanda mallam Ja'afar ya hadu da shi a makkah ya nuna masa wannan akida da yake so ya kafa mutane a kai ba daidai ba ne ya rantse da Allah cewar wadannan mutanan ba dalibansa ba ne ya kara da cewa shi bai san su ba sai mallam ja'afar mahmud adam ya ce indai kana son ka kubuta daga wannan aqida to ka dauki alkalin da zai rubuta da yawunka kai ka kubuta daga wannan aqida da ake jingina ka da ita haka muhammad yusuf ya sa aka samo alkalin da suke cewa aikin boko haramun ne shine yayi masa rubutu da yaran da ake cewa haramun ne akayi har ,muhammad yusuf yasamu yadawo najeriya daga baya ya nuna wa duniya shi yana nan akan bakan sa na nunawa duniya cewa yin karatun boko haramun ne.

Muhammad Yusuf Muhammad Yusuf
1. Leader of Boko Haram (en) Fassara

2002 - 30 ga Yuli, 2009 - Abubakar Shekau
Rayuwa
Haihuwa Jihar Yobe, 29 ga Janairu, 1970
ƙasa Najeriya
Mutuwa Maiduguri, 30 ga Yuli, 2009
Yanayin mutuwa  (extra-judicial killing (en) Fassara)
Ƴan uwa
Yara
Sana'a
Sana'a Mai da'awa
Aikin soja
Ya faɗaci Rikicin Boko Haram
Imani
Addini Musulunci

Tarihi

Yusuf wanda aka haifa a kauyen Girgir, a cikin Jakusko, jihar Yobe ta yanzu, a Najeriya, ya sami ilimi a gida, wato a ƙasa Najeriya, musamman ma a Borno. A farkon rayuwar shi ya fara shi'anci ne, daga baya ya tuba ya koma salafiyyanci, Daga baya ya kara karatun addinin Musulunci kuma ya zama dan Salafiyya. inda a gab da karshan rayuwar sa shugaban salafiyya na Najeriya mai suna Muhammad Auwal Albani Zaria ya barran ta da shi, bayan jin akidar shi na Boko Haram.

Karatu

A cewar wani masani Paul Lubeck na Jami'ar California da ke Santa Cruz, a lokacin da yake saurayi Yusuf an koyar da shi Shi'a a karkashin jagoran cin Ibrahim Zakzaky. daga baya yace ya tuba ya koma Ahlus-Sunnah, inda ya kulla alaka da Salafiyya, kuma yace yana bin koyarwar Ibn Taimiyya . Yana da kwatankwacin karatun digiri na biyu, a cewar wani malami dan Najeriya Hussain Zakaria. Yusuf bai taɓa kwarewa sosai a Turanci ba kamar yadda aka ruwaito. Ya yi imani da aiki da shari'ar Musulunci sosai, wanda ke wakiltar abin da ya dace da shi na adalci bisa koyarwar annabin Islama, Muhammad.(SAW) Mayakan Boko Haram za su kashe membobin wasu kungiyoyin Musulmi kamar kungiyar Izala ta Salafist da 'yan kungiyar Sufi Tijjaniyya da Qadiriya. A cikin hirar da yayi tare da BBC, wacce ta yi da shi a shekarar 2009, Yusuf ya bayyana imaninsa cewa batun ilmi kan cewa duniyan da ke zagaye da sararin samaniya ya saba wa koyarwar Musulunci kuma ya kamata a yi watsi da shi . Ya kuma yi watsi da juyin halittar masanin kimiyya mai suna Darwin, da kuma batun kewayen halittar da ke samar da ruwan sama. A cikin hirar harma ya ce:

Error: No text given for quotation (or equals sign used in the actual argument to an unnamed parameter)

— "Akwai wasu fitattun masu wa'azin addinin Islama da suka gani kuma suka fahimta cewa ilimin zamani irin na Yammacin Turai ya gauraya da batutuwan da suka saba wa abin da muka yi imani da shi a Musulunci," in ji shi.

Error: No text given for quotation (or equals sign used in the actual argument to an unnamed parameter)

— "Kamar ruwan sama . Mun yi imani halittar Allah ce maimakon kazamar ruwa da rana ta haifar wanda ke tattarawa kuma ya zama ruwan sama.

Error: No text given for quotation (or equals sign used in the actual argument to an unnamed parameter)

— "Kamar faɗin duniya yanki ne . Idan ta ci karo da koyarwar Allah, sai mu ki shi. Mun kuma ki yarda da ka'idar Darwiniyanci."

Akida

kamar yadda wani masani a harkan ta'addanci mai suna Paul Lubeck na Jami'ar Kalifoniya ya fada, yace Muhammad Yusuf a lokacin kuruciyar sa ya fara bin akidar Shi'a ne a karkashin jagoranci Ibrahim Zakzaky, wanda daga baya yace ya tuba, daga bisani sai ya koma akidar Salafanci, inda ya fara karatu a karkashin Albani Zaria da Ja'afar Mahmud Adam, kuma yana bayyana cewa yana bin koyarwar Shehin Musulunci mai suna Ibn Taymiyyah, bayan ya bayyana akidar sa na cewa Boko Haramun ne sai Albani Zaria da Ja'afar Mahmud Adam suka barran ta da shi, kuma suka yi masa wa'azi gami da raddi.

An ruwaito cewa bai iya turanci ba, amma manazarta ilimin sun karyata hakan, rahotanni sun tabbatar da cewar yana yin Turanci sosai,sannan ya iya larabci daidai gwar gwado kuma yakasance me halartar karatun mallam ja'afar mahmud adam

Kafa gungiya

Muhammad Yusuf ne ya fara da'awan kungiyar mai suna da larabci Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad, wanda a larabci yake nufin "Al'umma masu bin Sunna, masu da'awa da jihadi ". Musulmi ne kuma dan Najeriya wanda ya kafa kungiyar Boko Haram a shekara ta 2002. Shine ya zama shugaban ta har izuwa lokacin da ya rasa ransa a shekarar 2009. Asalin sunan kungiyar ita ce Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad

Mutuwa

Bayan rikicin Boko Haram na watan Yulin 2009, sojojin Najeriya suka kama Yusuf a gidan surukin sa, daga baya sun mayar da shi hannun rundunar yan sandan Najeriya. 'Yan sanda sun kashe Yusuf a gaban jama'a a gaban hedkwatar' yan sanda na Maiduguri . Jami'an 'yan sanda da farko sun yi ikirarin cewa an harbe Yusuf ne a yayin da yake kokarin tserewa, ko kuma ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu a yayin artabu da sojoji.

Rayuwar shi

Yusuf yana da mata hudu da ‘ya’ya 12, daya daga cikinsu shi ne Abu Musab al-Barnawi, wanda ya yi ikirarin cewa shine shugaban Boko Haram tun shekarar ta 2016 a matsayin sahihin shugaban kungiyar Boko Haram, yana adawa da Abubakar Shekau. An ba da rahoton cewa yana rayuwa na jin dadi, wanda ya haɗa da mallakan kayan alatu, irin su Mercedes-Benz, wayar hannu da kuma Komfuta.

Diddigin bayanai na waje

Manazarta

Tags:

Muhammad Yusuf TarihiMuhammad Yusuf KaratuMuhammad Yusuf AkidaMuhammad Yusuf Kafa gungiyaMuhammad Yusuf MutuwaMuhammad Yusuf Rayuwar shiMuhammad Yusuf Diddigin bayanai na wajeMuhammad Yusuf ManazartaMuhammad YusufAbubakar ShekauBoko HaramCadiKamaruMaiduguriNajeriyaNijarTa'addanci

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

PakistanShehu Hassan KanoJikokin AnnabiAccraQatarJerin kasashenYunus IdrissiDuniyaJerin Sarakunan KanoBashir Bala CirokiDokaBayelsaNijar (ƙasa)Ali KhameneiAman Anand SinghJerin Sunayen 'yan majalisar wakilan Najeriya, 2019–2023Ciwon Daji Na BakaFrancette Razafindrakoto HarifanjaJerin Ƙauyuka a jihar NejaJam'iShams al-Ma'arifMal Samaila SuleimanMurja IbrahimMansura IsaƳancin mallakar hannun jariJerin shugabannin ƙasar NijeriyaIraƙiRuwan BagajaShayiArewacin NajeriyaMaryam Musa WaziriIsra'ilaAbubakar Shehu-AbubakarBankin DuniyaOrder of the British EmpireMatan AnnabiRabi'u Musa KwankwasoTsarin DarasiJerin ƙauyuka a jihar JigawaJerin Ƙauyuka a Jihar KatsinaArmeniyaMasarautar Sarkin Musulmi, SokotoHaboBangladeshMiyar tausheManhajaMax AirAli Modu SheriffGabonOmkar Prasad BaidyaTwitterAl Kur'aniMomee GombeTarayyar AmurkaJerin SahabbaiShehu ShagariWurnoHawainiyaBidiyoLarabciJa'afar Mahmud AdamZaben Gwamnan Jihar Kano 2023KasuwanciBasirTuraiJerin ƙauyuka a Jihar GombeMasarautar Gombe🡆 More