Falalar Azumi Da Hukuncinsa

Ma’anar kalmar Azumi a larabci Kamewa da barin wani abu Ma’anar Azumi a Shari’a Shi ne bautawa Allah ta hanyar kamewa daga cin abinci da abin sha da jima’i, tun daga hudowar alfijir har zuwa faduwar rana.

Falalar Azumi

Azumi yana da falala mai girma, da lada mai yawa. Allah Madaukakin Sarki ya raba azumi zuwa gare shi, saboda girmama shi da daukaka shi. Ya zo a cikin hadisi qudusi daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ya ce, “Dukkan aikin da dan Adam ana kan kare masa shi, ana ninka kyakkyawa sau goma, har zuwa ninki dari bakwai. Allah Mai girma da buwaya ya ce, “Sai dai azumi, haqiqa shi nawa ne, ni ne nake ba da ladansa, mutum yana barin sha’awarsa da abincinsa saboda ni. Mai azumi yana da farin cikin biyu, farin ciki yayin buda bakinsa, da farin ciki yayin haduwa da Ubangijinsa. Warin bakin mai azumi ya fi almiski qanshi a wurin Allah” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Hikimar Shar’anta Azumi

1 – Tabbatar da tsoron Allah, wajen amsa wa umarninsa, da biyayya ga shari’arsa. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “(An wajabta muku azumi ne) ko kwa samu tsoron Allah” (Albaqara : 183).

2 – Saba wa kai haquri, da qarfafa wa zuciya wajen danne sha’awa.

3 – Saba wa mutum da kyautatawa, da jin tausayin mabuqata da talakawa, saboda idan mutum ya xanxani yunwa zuciyarsa za ta yi laushi ta karkata zuwa ga mabuqata.

4 – Samun hutu a jiki da samun lafiya a cikin azumi.

Hukuncin Yin Azumi

Azumin da Allah ya shar’anta ya kasu zuwa ga:

1 – Azumin Wajibi Ya kasu gida biyu :

A – Azumin da Allah ne ya wajabta a kan bawa tun da farko, shi ne azumin watan Ramadan, kuma rukuni ne daga rukunan musulunci. B – Azumin da bawa ne yake musababin wajabata wa kansa shi, kamar azumin kaffara.

2 – Azumin Mustahabbi,

Shi ne dukkan azumin da shari’a take so a yi shi, kamar azumin ranar Litinin da Alhamis, da azumin kwana uku a kowane wata, da azumin ranar Ashura, da azumin goman farko a cikin watan Zulhijjah, da sittu Shawwal da azumin ranar Arfa.

Sharuddan Wajabcin Azumi

1 – Musulunci : Azumi ba ya wajaba a kan kafiri.

2 – Balaga : Azumi ba ya wajaba a kan yaro qarami, sai dai za a umarce shi da yi idan zai iya, don ya saba.

3 – Hankali : Azumi ba ya wajaba a kan Mahaukaci.

4 – Samun Iko : Azumi ba ya wajaba a kan wanda ba zai iya yi ba.

Azumin Watan Ramadan

Azumin watan Ramadan rukuni ne daga rukunan musulunci, kuma farilla ne da Allah ya farlanta a kan bayinsa. Allah Maxaukakin Sarki ya ce , “Ya ku waxanda suka yi imani an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta wa waxanda suke gabaninku don ku samu taqawa”. (Al-Baqarah: 183) Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ya ce, “An gina musulunci a bisa ginshiqai biyar” [Buhkari ne ya rawaito shi]. Sai ya ambaci “Azumin watan Ramadan” daga cikinsu.

Daga Cikin Falalar Watan Ramadan

1 – A watan Ramadan Ana bude qofofin Aljannah, ana rufe qofofin wuta, ana daure Shaidanu, zuciya tana fuskantar aikin alheri. Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ya ce, “Idan Ramadan ya zo, sai a bude qofofin sama, a rufe qofofin Jahannama, a daure Shaidanu” . [Buhkari ne ya rawaito shi]

2 – Yin azumi da tsayuwar sallar asham saboda Allah da neman lada yana gafarta abin da ya gabata na zunubai. Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ya ce, “Wanda ya yi azumin watan Ramadan, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]. Ya sake cewa : “Wanda ya yi tsayuwar sallah a watan Ramadan, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa” . [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

3 – A cikin watan Ramadan Akwai daren Lailatul Qadri, wanda Allah yake cewa a kansa “Daren lailatul Qadri ya fi wata dubu alheri” . (Alqadr : 3) Duk wanda ya tsaya a cikin wannan dare yana mai imani da Allah da neman lada to za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa. Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ya ce, “Wanda ya tsaya a daren lailatul Qadri yana mai imani da Allah da neman lada to za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi] .

4 – Umara a cikin Ramadan tana daidai da yin aikin hajji tare da Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ). Manzon Allah ya ce, “Umara a cikin Ramadan tana daidai da aikin hajji tare da ni” [Muslim ne ya rawaito shi]

5 – Watan Ramadan watan Alqur'ani ne, a cikinsa aka saukar da shi, don haka ya dace a yawaita karanta shi a cikin wannan wata. Allah ya ce, “Watan Ramadan wanda aka saukar Alqur'ani a cikinsa, Shiriya ne ga mutane, da ayoyin bayanannu da rarrabe wa tsakanin qarya da gaskiya” (Albaqara : 185) .

6 – Watan Ramadan wata ne na kyauta da ciyarwa da sadaka. An karvo daga Abdullahi dan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “ Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ya fi dukkan mutane kyauta, ya kasance lokacin da yafi kyauta shi ne a cikin Ramadan, lokacin da Mala'ika Jibrilu yake haduwa da shi. Mala’ika Jibrilu yana haduwa da shi a kowane dare a cikin Ramadan, ya yi karatun Alqur'ani tare da shi. Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ya fi kowa kyauta lokacin da Mala'ika Jibriru yake hadu da shi, ya fi iska sakakkiya kyauta” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]. ==Da me Ake Tabbatar Da Kamawar Watan Ramadan?== Watan Ramadan ya tabbata da ganin wata, idan aka ga wata bayan faduwar ranar ashirin da tara ga watan Sha’aban, to watan Ramadan ya kama, idan kuwa ba a ga wata ba, bayan faduwar ranar ashirin da tara ga watan Sha’aban, ko kuma wani abu ya hana ganinsa, kamar hadari, ko qura, ko hayaqi, to sai a cika lissafin watan Sha’aban kwana talatin. Saboda fadin Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) : “Ku yi azumi don ganin wata, ku sauke don ganinsa, idan an kare muku shi, to ku cika Sha’aban kwana talatin” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi] .

Karya Azumi

Karya azumi haramun ne, kuma yana daga cikin manya-manyan laifuka. Duk wanda ya karya azumin na rana daya ba da wani uzuri ba, kuma bai tuba ba, to babu abin da zai isar masa, koda ya yi azumin zamani gabadaya. Saboda fadin Annabi ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) “Duk wanda ya karya azumi rana xaya daga Ramadan, ba a a kan wani rangwame da Allah ya yi masa ba, to azumin zamani gabadaya ba zai rama masa ba” [ Abu Dawud ne ya rawaito shi] . Azabar wanda ya karya azumi da gangan mai girma ce. An karvo daga Abu Umamata Al-bahili – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Na ji Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) yana cewa, ina cikin barci, sai wasu mutane biyu suka zo min,…..sannan suka tafi da ni, sai kawai na ga wasu mutane an rataye su ta agararsu, muqamuqansu a tstssage, jini yana ta kwarara. Sai ya ce, na ce, su wanene wadannan? Sai ya ce, Wadannan sune wadanda suke karya azumi ne tun kafin lokacin shan ruwa ya yi” [Ibn Hibban ne ya rawaito shi] .

Manazarta

Tags:

Falalar Azumi Da Hukuncinsa Falalar AzumiFalalar Azumi Da Hukuncinsa Hikimar Shar’anta AzumiFalalar Azumi Da Hukuncinsa Hukuncin Yin AzumiFalalar Azumi Da Hukuncinsa Sharuddan Wajabcin AzumiFalalar Azumi Da Hukuncinsa Azumin Watan RamadanFalalar Azumi Da Hukuncinsa Daga Cikin Falalar Watan RamadanFalalar Azumi Da Hukuncinsa Karya AzumiFalalar Azumi Da Hukuncinsa ManazartaFalalar Azumi Da Hukuncinsa

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Kogin HadejiaHamza al-MustaphaIsaBudurciHannatu MusawaJean-Luc HabyarimanaBakar fataKubra DakoGaɓoɓin FuruciSa'adu ZungurKarayeRakiya MusaSaudiyyaJerin Gwamnonin Jahar SokotoGhanaKuɗiSallar NafilaShabnim IsmailYahaya BelloCartier DiarraJerin sunayen Allah a MusulunciTarihin falasdinawaMata TagariAli NuhuTurkiyyaMu'awiyaRoger De SáAskiMustapha Ado MuhammadUkraniyaYammacin AsiyaIvory CoastAdolf HitlerSunnahMurja IbrahimKannywoodMadinahHauwa WarakaBruno SávioCharles RepoleAl Kur'aniTarihin HabashaJahar TarabaSallar Idi BabbaBasirHussaini DankoArewacin NajeriyaWakilan Majalisar Tarayyar Najeriya Daga SokotoJerin ƙauyuka a jihar KebbiJerin Gwamnonin Jihar ZamfaraJerin Sarakunan Musulmin NajeriyaJerin kasashenSadi Sidi SharifaiƘungiyar Ƴantar da MusulmaiBornoA Tribe Called JudahAbba Kabir YusufSudanAnnabi SulaimanDahiru Usman BauchiCadiMaryam Abubakar (Jan kunne)Tarayyar TuraiMaryam BoothKimiyyaMasarautar KontagoraAbida MuhammadIranBirtaniyaTaimamaAba OgunlereShari'a🡆 More