Mata Tagari

MACE TAGARI !!!

Mata Tagari

.

Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “Duk wanda ALLAH Ya azurta shi da Mace tagari hakika ALLAH Ya taimake shi da rabin addinin shi, sai yaji tsoron ALLAH wajen samun sauran rabin addininsa.” [Sahihut-Targib: 1916]

.

Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “Duniya kayan jindadi ne, amma mafi alkhairin abun jindadi acikinta shine Mace Tagari.” [Muslim]

.

Manzon ALLAH (ﷺ) Yana cewa: “Mumini bai amfanuwa da wani abu bayan tsoron ALLAH ba abunda yafi alkhairi fiye da Mace Tagari, idan ya umurce ta sai tayi masa biyayya, idan kuma ya kalleta sai ta faranta masa rai, idan kuma yayi rantsuwa akanta sai ta kubutar dashi, idan kuma baya tare da ita sai ta kiyaye akan kanta da dukiyarsa.” [Sahih Ibn Mâjah: 1857]

.

Sheikhul Islam Ibn Taimiyya (Rahimahullah) Yace: "Mace tagari tana kasancewa ne cikin abota da mijinta shekaru masu yawa, ita abin jindadinsa ce, wacce Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “duniya kayan jindadi ce, mafi alkhairin abin jindadinta itace mace-mumina, idan ka kalleta sai ta kayatar dakai, idanka bata umarni sai tabi umarninka, idan ka buya ga barinta sai ta kiyaye maka kanta da kuma dukiyarka.”

.

Itace wacce Annabi (ﷺ) yayi umarni (da a aura) acikin fadinsa yayin da Almuhajirun (mutanen Makkah da sukai hijira zuwa madina) suka tambayeshi cewa wacce irin dukiya zamu rika (nema) Sai Yace: dayanku ya riki zuciya mai godiya (ga ALLAH), dakuma harshe mai yawan ambaton (ALLAH), da kuma mace mumina, zata taimakeshi wajen samun lahira." [Saheehul Jami'i na Albany (5355)]

.

Sai ya kasance ansamu kauna da Rahama kamar yanda ALLAH Madaukakin sarki ya ambata a cikin littafinsa (Alqur'ani), sai ya kasance radadin rabuwa (yayinda mijin ya nisanceta) shiyafi tsanani daga mutuwa, wani lokacin ma shiya fi tsanani idan aka hada shi da sarayar dukiya, shiya fi tsanani da rabuwa da gari, musamman ma idan yakasance akwai alaka daya daga cikin abokin zamansa (a aure), ko kuma akwai yara atsakaninsu.” [Majmoo'ul Fatawa (35/299]

.

Sheikh Ahmad Bin Yahya Bin Muhammad Annajmeey (Rahimahullah) Yace: “Shi namiji yanayinsa (kimarsa) bata cika kuma rayuwa ba zata masa dadi ba sai da Mace tagari, kuma Mace ba zata samu nutsuwa ba hakanan rayuwa ba zata mata dadi ba sai da miji nagari.” [Ta'asisul Ahkaam 4/172]

.

★SHAWARA: Idan kana bukatar samun Mace Tagari Toh lallai kayi kokari kai ma ka zamo Nagari, haka kema idan kina bukatar samun Miji nagari Toh kiyi kokari ki zamto mace tagari, kunga idan kuka hadu a Lambun inuwar soyayya sai kuyi ta haihuwar 'Ya'ya Nagari da yardar ALLAH.

.

Mata Tagari

ALLAH Ya sanya mu cikin bayinsa nagartattu kuma Ya azurtamu da abokan zama Nagari (Ameen)

Tags:

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Vincent van GoghAzareBushiyaJerusalemHadiza MuhammadGodwin EmefieleKoriya ta KuduMohammed Danjuma GojeHaɗejiyaHausaSiriyaTogoDambeKanunfariAlhassan DoguwaMunafiqNelson MandelaJapanIbrahim ibn Saleh al-HussainiAbdussalam Abdulkarim ZauraMaryam Malika1978Al-BakaraSikhShehu SaniAliyu Ibn Abi ɗalibMasarautar BauchiMuhammad Al-BukhariJerin gidajen rediyo a NajeriyaCristiano RonaldoSafinatu BuhariSoyayyaPeruTarihin HausawaUba SaniMaltaSabon AlkawariKaduna (jiha)Sana'o'in Hausawa na gargajiyaTurkanciBola TinubuBashir Usman TofaMasarautar KanoBayelsaWSojaJavaFezbukDJ ABMasarautar KatsinaJahar TarabaPatrick Ibrahim YakowaKazakhstanYahaya BelloZaben Najeriya na 2023Jerin ƙauyuka a jihar YobeCukuMasarautar NajeriyaZheng HeAbd al-Rahman ɗan AwfJikokin Annabi Muhammadu, ﷺMicrosoft WindowsƘur'aniyyaBabban shafiMuhammad ibn Abd al-WahhabEmailMagana Jari CeLarabawaGashuaManzanniLIraƙiShi'aMansa MusaAbubakar🡆 More