Birgediya Janar Harris Otadafevwerha Deodemise Eghagha (An haife shi a ranar 8 ga Maris, 1934) an nada shi gwamnan soja a jihar Ogun, Najeriya daga Yuli 1978 zuwa Oktoban 1979 a lokacin mulkin soja na Janar Olusegun Obasanjo, inda ya mika mulki ga zababben gwamna Olabisi Onabanjo a farkon watan Oktoba.
Jamhuriyar Najeriya ta Biyu.
Harris Eghagha | |||
---|---|---|---|
ga Yuli, 1978 - Oktoba 1979 ← Saidu Ayodele Balogun - Olabisi Onabanjo → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Okpe, 8 ga Maris, 1934 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Urhobo (en) | ||
Mutuwa | 19 ga Maris, 2009 | ||
Karatu | |||
Harsuna | Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da hafsa | ||
Digiri | Janar |
An haifi Eghagha a ranar 8 ga Maris, 1934 a Mereje, karamar hukumar Okpe, Urhoboland, jihar Delta .
Eghagha ya taka rawa kadan a juyin mulkin watan Janairun 1966 wanda aka hambarar da jamhuriya ta farko a Najeriya kuma ya Haifar da mulkin soja na Manjo-Janar Johnson Aguiyi-Ironsi a matsayin Lieutenant na biyu mai kula da shinkan gen hanya a Kaduna.
An nada shi gwamnan soja a jihar Ogun, Najeriya a Ranar Yuli, 1978 zuwa Oktoban 1979. Yasamu Nasarorin da ya samu a lokacin dayake gwamnan jihar Ogunsun hada da gina rukunin majalisa da hanyoyin sadarwa a Abeokuta, babban birnin jihar. Ya gina tare da kaddamar da Otal din Jihar Ogun, Abeokuta, ya kafa masana’antu a fadin jihar sannan ya kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ogun (yanzu Moshood Abiola Polytechnic ) a Abeokuta. Ya kuma rike mukaddashin Gwamnan Jahohin Sokoto da Kwara, kuma ya kasance Babban Kwamishinan Najeriya a Ghana.
Birgediya Janar Harris Eghagha ya rasu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas a ranar 19 ga Maris, 2009 yana da shekaru 75.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Harris Eghagha, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.