Aliyu Sani Madakin Gini

Aliyu Sani Madaki (An haife shi a ranar 15 ga watan Junairu shekarata alif 1967) a karamar hukumar Dala dake jihar Kano a arewacin Najeriya.

Haihuwa da Karatu

An haifi Aliyu Sani Madaki ranar 15 ga watan Junairu 1967 a garin Dala dake jihar Kano a Najeriya.

Hon. Madaki ya halarci Makarantar Sakandare ta Gwamnati Gwammaja, Kano inda ya samu shaidar kammala sakandare ta yammacin Afrika (WAEC) a shekarar 1984. Ya wuce Kano State Polytechnic inda ya sami Difloma ta kasa (OND) a shekarar 1987. A lokacin da yake karatu a Kano State Polytechnic. ya kasance shugaban kungiyar dalibai (SUG). Ya halarci Makarantar Koyon Fasaha ta Tarayya (Federal Polytechnic Mubi) inda ya karanta Accounting sannan ya kamala digiri na biyu (HND) a shekarar 1987. A shekarar 2015, ya sami digiri na MBA a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi.

Aiki

Aliyu Sani Madaki ya yi aiki a matsayin akawu a ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya Abuja daga shekarar 1991 zuwa 2001. Sannan ya kasance babban akawunta a ma’aikatar kudi ta tarayya daga 2001 zuwa 2002. A tsakanin 2002 zuwa 2006 ya kasance mataimakin shugaban akawuntan kudi a ma’aikatar kudi ta tarayya. Ma'aikatar Wutar Lantarki da Karfe ta Tarayya. A shekarar 2006 Aliyu ya Ajiye aikin gwamnati inda yakoma rike kamfaninsa mai Suna Madakin gini consults Daga 2007 zuwa 2011 ya kasance Manajan Daraktan Madakin Gini Consults.

Siyasa

A shekarar 2007 Aliyu ya shiga harkar siyasa sosai Inda yayi Takarar majalisar tarayya a karkashin tutar Jam'iyyar AC Amma baiyi Nasara ba.

A shekara ta 2011 ne Madaki ya kuma tsayawa takara a Jam'iyyar PDP inda ya lashe kujerar Dan Majalisar Tarayya Mai wakiltar Karamar Hukumar Dala 2011-2015. Daga 2011 zuwa 2015, ya yi aiki a kwamitocin majalisar kamar haka; Housing, Appropriations, Legislative Budget & Research, (Mataimakin Shugaban), Cibiyoyin Lafiya, Harkokin Waje, da kuma Banking & Currency.

An sake zabe shi a shekarar 2015 a karkashin jam’iyyar All Progressive (APC) 2015-2019 Kuma ya tsaya takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a shekarar 2019 a karkashin tutar jam'iyyar PDP. Inda yayi rashi nasara a hannun Abokin Takarar sa Tsohon gwamnan Jahar Kano Malam Ibarahim shekarau.

Manazarta

Tags:

Aliyu Sani Madakin Gini Haihuwa da KaratuAliyu Sani Madakin Gini AikiAliyu Sani Madakin Gini SiyasaAliyu Sani Madakin Gini ManazartaAliyu Sani Madakin GiniDala

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

KashiHamisu Breaker2012AzerbaijanJoy IrwinMata TagariMignon du PreezTuranciShugabanciMartin Luther KingMaganiCutar AsthmaGwarzoShehu ShagariYareGudawaTarihin AmurkaJerin Ƙauyuka a Jihar KatsinaMaɗigoLarabaFloridaSallar NafilaKalaman soyayyaJerin shugabannin ƙasar NijarWataShams al-Ma'arifWasan BidiyoMatan AnnabiDahiru Usman Bauchin5exnIbrahim NarambadaAba OgunlereCarles PuigdemontShekaraEnioluwa AdeoluwaIngilaHauwa MainaAliyu Ibn Abi ɗalibHabbatus SaudaBornoNondumiso ShangaseAmaryaKabejiKos BekkerMuhibbat AbdussalamBayanauSallar Matafiyi (Qasaru)MadobiBobriskyAhmed MusaMiguel FerrãoAlbani ZariaYanar gizoJerin Sarakunan KanoFarautaKundin Tsarin Mulkin NajeriyaCiwon Daji Na BakaIsaFrancis (fafaroma)GoogleMasarautar GombeDaouda Malam WankéNahawuAzman AirJerin ƙauyuka a jihar KadunaNonoMutanen NgizimItofiya🡆 More