Kofar Marusa tana ɗaya daga cikin kofofin dake cikin birnin Katsina.Ta kofar ne Marusan katsina y biyo zuwanshi katsina.
Kofar Marusa |
---|
An gina kofar Marusa a wajen karni na Shabiyar 15 ne. Lokacin da aka gina sauran ganuwowin jihar Katsina, kuma ta samo asalin sunanta ne daga wani Basarake na Habe da ke mulkin Dutsi a wannan lokacin, wanda ake kira da Marusa Usman. Ta wannan kofar ce Marusa din ke bi in zai tafi Dutsi, ta nan ne kuma yake shiga idan ya dawo. Daga nan ne aka sanya ma kofar sunan Basaraken ta zama kofar Marusa Usman. Kofar Marusa, ta yi makwabtaka da wasu unguwanni da ke cikin kofar.
Akwai dai unguwar Kerau daga cikin ta wanda shekarunta ba su wuce sitinba 60 da kafuwa ba, koda yake, a da can, tun lokacin mulkin Habe har ya zuwa na Dallazawa, an yi wani wuri da ake kira unguwar Dantura, wanda a halin yanzu babu wannan unguwa saboda Kerau ta hade ta, ta koma cikin Kerau din. Sai ita kanta kofar marusan da sauransu...
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Ƙofar Marusa, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.