Ahmad Gumi: Malamin Addini

Ahmad Abubakar Gumi ko Ahmad Gumi, ko mufti, ɗa ne ga daya daga cikin shahararrun malaman Sunna a Arewacin Najeriya marigayi Shaykh Abubakar Mahmud Gumi.

Ahmad Gumi: Farkon rayuwa, Ilimi, Aikin soja Ahmad Gumi
Rayuwa
Haihuwa Kaduna, 1959 (64/65 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Mutanen Fulani
Ƴan uwa
Mahaifi Abubakar Gumi
Karatu
Harsuna Turanci
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a mufti (en) Fassara da Malamin addini
Imani
Addini Mabiya Sunnah

Farkon rayuwa

An haifi Ahmad Abubakar Gumi a shekara ta alif dari tara da hamsin da tara 1959. Ya kasance ɗa ne ga malam Abubakar Mahmud Gumi kuma shi ne babban ɗan sa wanda mahaifiyarsa ita ce Amina Abubakar Gumi kuma uwargida ce a cikin mata uku da malamin ya aura.

Ilimi

Ahmad Abubakar Gumi yafara makarantar sa ta farko a cikin garin Kano, inda daga bisani ya dawo jihar Kaduna ya halarci Kwalejin [[Kwalejin Tunawa da Sardauna]] (Sardauna Memorial College (SMC)) don gudanar da karatun babbar sakandire, sannan bayan ya kammala karatun sa, ya samu shiga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya don yin karatun Likitanci, bayan kammala karatun sa ya sa ya shiga Kwalejin Tsaron Najeriya, inda ya fito amatsayin Sojan Najeriya. Gumi ya yi murabus daga aikin soja a matsayin Kaftin kuma ya koma Saudi Arebiya don ci gaba da karatunsa a fannin addinin Musulunci a Jami’ar Ummul al-Qura inda ya yi karatun Fiƙihu da Tafsiri inda yakai ga samun matakin karatu na digirin digirgir wato digiri mataki na uku (Ph.D) daga Jami'ar Ummul Qura dake Birnin Makkah a ƙasar Saudiya.

Ahmad Gumi ya kasance mai son ganin ƴan siyasa sun bi dokokin ƙasa wurin aiwatar da haƙƙoƙin da aka ɗauka masu na jama'a, abinda ya jawo wasu suke ganin malamin bai dace yana sanya kansa cikin batutuwan siyasa ba. A shekarun 2012 zuwa 2014 yayi suna wurin nuna matsalolin gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan. Kuma haka a baya bayan nan ana jinsa yana yawan janyo hankali game da mulkin shugaba Muhammadu Buhari bisa ga salon Mulkin sa da yadda bai kula da harkokin tsaron ƙasa.

Gwamnatin kasar Saudiyya ta taɓa kama shi a shekarar 2013 bisa zargin alaƙa da Umar Faruq Abdulmutallab wanda ya yi nufin tayar da ban a wani jirgin Amurka. Amma daga baya aka sallame shi bayan jami'ai sun wanke shi.

Aikin soja

Ya yi aiki a Kwalejin Tsaro ta Najeriya a matsayin jami'in soja, kuma ya yi ritaya a matsayin kyaftin.

Tuhuma

A ranar juma'ar 25 ga watan Juni, na shekarar 2021. Hukumar Department Of Security Service ( DSS) suka gayyace shi domin tuhumar sa da sukeyi akan alaqar sa da yan ta'adda da fulanin daji masu garkuwa da mutane. Inda yake samun su domin samun sulhu.

Manazarta

Tags:

Ahmad Gumi Farkon rayuwaAhmad Gumi IlimiAhmad Gumi Aikin sojaAhmad Gumi TuhumaAhmad Gumi ManazartaAhmad GumiArewacin NajeriyaShaykh Abubakar Mahmud GumiSunna

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

HankakaGamawaMasarautar DauraWanzanciEmmanuel E. UduaghanKankanaSunayen RanakuFati BararojiMisraVKano (jiha)RashaUkraniyaOgbomoshoShukaKiyawaKhalid ibn al-WalidTauraron dan adamKamal AbokiMuhammad YusufDiego MaradonaObot-AkaraAttahiru BafarawaAli NuhuDogecoinYan takarar gomna na katsina a zaben 2023Ibn Qayyim al-JawziyyaWasanniSarakunan Gargajiya na NajeriyaIsah Ali Ibrahim PantamiAyesha GaddafiShehu ShagariMuhammad Bello YaboAbdullahi ɗan AbbasJalingoIsaUsman Dan FodiyoSoyayyaDorothy A AtabongSaharaAhmed Ibrahim LawanKaruwanci a NajeriyaMajalisar Dokokin Jihar AdamawaFrançois FillonAl'adaAbdulsalami AbubakarKabiru GombeAnnabi MusaMadinahPeoples Democratic PartyBauchi (birni)Abubakar RimiMaliPatience JonathanMuhammad Inuwa YahayaSallar NafilaNamadi SamboGumelShuwakaKubauBilkisu ShemaKauruAlex Ifeanyichukwu EkwuemeLabarin kasa na NijeriyaSha'aban Ibrahim SharadaAfirka ta KuduKimiyyaJerin ƙauyuka a jihar KanoTudun Wada🡆 More