Masarautar Karaye masarauta ce a jihar Kano mai hedikwata a garin Ƙaraye.
Sarkin Ƙaraye na yanzu shine Alhaji Dr. Ibrahim Abubakar II.
Masarautar Ƙaraye | ||||
---|---|---|---|---|
Emirate (en) | ||||
Bayanai | ||||
Farawa | 2019 | |||
Ƙasa | Najeriya | |||
Babban birni | Karaye | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jiha | jihar Kano |
Garin Ƙaraye hedikwatar masarautar Ƙaraye ce kuma tana yammacin birnin Kano. Tun kafin zuwan Bagauda a shekarar 999, Magurguji ke zaune a Karaye. An kafa garin Ƙaraye a shekara ta 1085. Daga shekarar 1101 zuwa 1793, sarakunan Habe sun yi sarautar Ƙaraye. A zamanin sarakunan Habe, masarautar Karaye ta kara faɗaɗa zuwa yankin Yamma da Arewacin Jihar Kano da ke yanzu.
A lokacin da Majalisar Bagauda ke mulki a Kano sun nemi haɗin kan maƙwabciyarsu Masarautar Karaye domin haɗa ƙarfi da ƙarfe domin kare kansu daga wasu masarautu irinsu Zariya da Katsina da Sakkwato . Ƙaraye ta amince ya bada hadin kai da gidan Bagauda inda Ƙaraye ya koma masarautar Kano . Daga lokacin da Karaye yake ƙarƙashin masarautar Kano har zuwan Sarakunan Fulani bayan Jihadin Usman Dan Fodio.
Masarautar Ƙaraye ta ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin Daular Kano har zuwa shekarar 2020 lokacin da gwamnatin jihar Kano ta fitar da wasu sabbin masarautu guda biyar tare da sauya tsarin masarautar Kano. A wancan lokacin gwamnatin Kano ta dawo da sabuwar Masarautar Karaye. Masarautar Ƙaraye ta ƙunshi ƙananan hukumomi takwas na jihar Kano, Karaye, Rogo, Gwarzo, Kabo, Rimin Gado, Madobi, Kiru da Shanono.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Masarautar Karaye, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.