Yakolo Indimi

Yakolo Indimi (an haifeta ranar 19 ga watan Maris, 1977) kuma an santa da Rahama Indimi ta kasance sananniyar yar kasuwa kuma mai taimaka ma al'uma.

Ta kasance shugaba-(CEO) kuma wacce ta samar da gidauniyar Yakolo indimi. Ta kasance darakta ce a Oriental Energy Resources Limited kuma yanzu haka darakta ce a Oriental OML 115. kuma ta kasance wacce ta ci lambar girma na duniya a shekarar 2019.

Yakolo Indimi Yakolo Indimi
Rayuwa
Haihuwa 19 ga Maris, 1977 (47 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa, Mai tsara tufafi da business executive (en) Fassara

Farkon rayuwa

An haifi Yakolo Indimi ne a Maiduguri, dake jihar Borno a shekarar alif 1977, ta kasance ƴar shahararran ɗan kasuwa Mohammed Indimi da kuma Hajiya Fatima Mustapha Haruna. Tayi karatu a makarantan University Primary dake Maiduguri. Ta yi karatun firamare a University Primary School, Maiduguri, a Jihar Borno sannan aka kai ta makarantar kwana a kasar Masar inda ta yi karantun sakandare boko da addini a El Nasr Girl College, da ke Alexandria, wadda ta kammala a 1989. Yakolo ta yi karartu a Jami’ar Lynn, Boca Raton da ke Florida a kasar Amurka. A nan ta yi digirina na farko a fannin kimiyyar aikin likitanci sannan ta yi digiri na biyu fannin gudunarwa na kasa da kasa.

Aiki

Bayan ta kammala yi wa kasa hidima a 2000, ta samu aiki kamfnin mahaifina na Oriental Energy Resources, inda ta yi aiki a sassa da kuma matakai daban-daban na tsawon shekara 20. Yanzu haka darekta ce rijiyar hakar mai ta OML 115. A shekarar 2010, ta shiga harkar ado da kwalliya inda ta bude kamfani mai suna Fashion Café, daga bisani ta sake samar wani kamfanin mai suna Devas Petal a shekarar 2015.

Ayyukan kyautatawa

Yakolo Indimi ta kafa gidauniya mai suna Yakolo Indimi Foundation, da manufar yaki da talauci, kawar da yunwa, isar da kayan agaji da samar da ayyukan kiwon lafiya ta hanyar samar da kudade da kayan tallafi ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa a sansanonin yan gudun hijirar da ke cikin Borno.

Lambar yabo

A shekarar 2019, Indimi ta samu lambobin yabo a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 74 da aka yi a birnin New York dake kasar Amurka, a bisa gudummawa da take bayarwa don cimma burin ci gaba mai dorewa (Sustainable Development Goals SDGs), a matakin na farko # 1 Babu

Manazarta

Tags:

Yakolo Indimi Farkon rayuwaYakolo Indimi AikiYakolo Indimi Ayyukan kyautatawaYakolo Indimi Lambar yaboYakolo Indimi ManazartaYakolo Indimi

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

David BiraschiSam DarwishLara GoodallAli ibn MusaGandun dajin Falgore na tara dabbobin dajiJamila HarunaJerin gidajen rediyo a NajeriyaHauwa MainaNonoUmmu SalamaTAJBankBincikeFuntuaAisha TsamiyaMaɗigoYankin Arewacin NajeriyaMurja IbrahimTutar NijarImam Malik Ibn AnasRuwaBeverly LangSarakunan Gargajiya na NajeriyaJerin ƙauyuka a jihar BauchiJerin yawan habakar mutane a jahohin NajeriyaShugabanciIsah Ali Ibrahim PantamiMalmoIbrahim ShekarauTalo-talo2009KimiyyaAliyu Mai-BornuBabban 'yanciTarihin Dangantakar Najeriya da AmurkaBarau I JibrinAminu Waziri TambuwalImaniƘananan hukumomin NajeriyaSautiAminu Sule GaroTarihin Kasar SinPidgin na NajeriyaKalabaƘarama antaLalleYahudanciAnnabi SulaimanMadobiSallahZakiCiwon hantaYanar gizoHauwa WarakaHausa BakwaiJimaJerin shugabannin ƙasar NijarHadisiEleanor LambertCristiano RonaldoOmkar Prasad BaidyaFassaraJerin Sunayen Gwanonin Jihar SokotoTekuMansura IsahSoGambo SawabaCutar AsthmaTarken AdabiBilkisu ShemaBirnin KuduCadibq93sJamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango🡆 More