Alakar Tarihin Hausa Da Bayajidda

Tarihi ya nuna cewa Bayajidda ya bayyana ne tsakanin karni na 16 zuwa na 19 amma kuma akwai shaidar kasancewarsa a al'adar Hausawa tun cikin karni na 9 zuwa na 10.

Sunansa na asali shi ne Abu Zaid. Amma saboda ba ya jin harshen Hausa sai aka sanya masa Ba-Ya-Ji-Da, wato ba ya jin Hausa a da.

Masana tarihi sun ce Bayajidda ne ya kashe wata macijiya a rijiyar nan ta Kusugu da ke Daura. Macijiyar a wancan lokacin ta addabi mutanen garin inda take hana su dibar ruwa.

Sau daya kacal suke samun damar jan ruwa a mako wato ranar Juma'a, saboda yadda wannan macijiya ta yi kaka-gida a wannan rijiya.

Duk da gargadin da aka yi masa, Bayajidda ya yi kokarin dibar ruwa a ranar Alhamis wato ranar da ba a dibar ruwa, a nan ne macijiya ta harzuko ta so hallaka shi, amma sai ya fille mata kai da takobinsa.

Daga baya ne sarauniya Daurama ta amince ta aure shi saboda bajintar da ya nuna.

An ce Bayajidda na da 'ya'ya uku, na farko shi ne Biram wanda ya haifa da 'yar sarkin daular Borno, sai kuma Bawo wanda ya haifa da Sarauniya Daurama na ukun kuma ya haife shi ne da wata kwarkwara.

Bawo ya haifi 'ya'ya shida kuma tare da kawunsu wato Biram su ne suka mulki garuruwan da ake kira Hausa bakwai wanda suka hada da Daura da Kano da Katsina da Zariya da Gobir da Rano da kuma Biram .

To sai dai farfesa Abdallah Uba Adamu, shugaban jami'ar koyo daga gida ta Najeriya, wanda masanin harshe da al'adun Hausawa ne ya ce "alakanta Hausawa da Bayajidda shafcin gizo ne."

Ya kuma ce "duk mutumin da ba shi da alaka da garuruwa guda bakwai da ke arewacin Najeriya, to ba Bahaushe ba ne. Sai dai a kira shi mai magana da yaren Hausa."

Garuruwan dai su ne birnin Kano da Katsina da Daura da Zazzau da Rano da Gobir da kuma Biram.

Farfesa Abdallah ya kuma yi watsi da batun da wasu manazarta ke fadi cewa Hausa yare ne ba kabila ba, a inda ya ce "Hausawa na da daulolinsu."

To sai dai martanin da farfesa Tijjani Muhammad Naniya na jami'ar Bayero ya yi game da wadannan kalamai na Farfesa Abdallah Uba, shi ne babu wani abu a duniya da ake zancensa ba tare da babu shi ba.

''Duk abin da ka ga ana maganarsa to akwai shi, zan yarda idan aka ce kila an yi karin gishiri, ko kuma an yi wani kuskure a ciki, amma ba wai ace babu shi dungurungum ba''.

Manazarta

Tags:

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

TarihiZaben Najeriya na 2023INomaNIbrahim ShemaCAbdulwahab AbdullahKatsina (birni)Masarautar NajeriyaHajaraIspaniyaIbn SinaMuhammadTauhidiMurtala NyakoTalo-taloTsibirin BamudaBBC HausaTarayyar SobiyetAdolf HitlerAbdullahi ɗan AbbasKhalid Al AmeriMalik Ado-IbrahimDan-MusaNairaJihar RiversHamisu BreakerAliyu Muhammad GusauFJerin gwamnonin jihar KatsinaHausa BakwaiBet9jaYakubu GowonTarihin Jamhuriyar NijarNiameyNelson MandelaUmmi RahabMasarautar KatsinaKawu SumailaFort AugustaborgYakubu LadoSenegalJerin ƙauyuka a jihar SakkwatoJakiBola IgeWAlwalaHannatu BashirKano (birni)BayelsaHassan Usman KatsinaArgentinaMuhammad ibn Abd al-WahhabAfro CandyMohammed Abdullahi AbubakarRashKampalaSiriyaLalleYobe2020IndiyaHawainiyaHalima DangoteDRamadanNaziru M AhmadShinkafaKitsoVanguard (Nigeria)Larabawa🡆 More