ä
An taskan ce wannan muƙalar a cikin jerin Muƙaloli_masu_kyau a Hausa Wiki Ana sa ran wata rana wannan muƙalar zata kasance a Babban Shafin Muƙalar mu a yau |
Ibrahim Shema | |||
---|---|---|---|
29 Mayu 2007 - 29 Mayu 2015 ← Umaru Musa Yar'Adua - Aminu Bello Masari → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Dass (Nijeriya), 22 Satumba 1952 (71 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Hausa | ||
Karatu | |||
Harsuna | Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Barista Ibrahim Shehu ShemaIbrahim Shehu Shema (Taimako·bayani) (An haife shi ranar 22 ga watan Satumba, shekara ta alif ɗari tara da hamsin da bakwai (1957) miladiyya. Lauya ne kuma ɗan siyasa ɗan Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Katsina da ke a arewa maso yammacin ƙasar a lokacin babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2007.
An sake zaɓen shi na tsawon shekaru huɗu a ranar 28 ga watan Afrilu, shekarar 2011, wanda ya yi dukkan takarar a ƙarƙashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP). Wa’adinsa na biyu a kan ƙaragar mulkin gwamnan jihar na shekaru huɗu ya ƙare ne, a ranar 29 ga watan Mayun shekara ta 2015, daga nan ya mikawa Aminu Bello Masari zaɓaɓɓen gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress Mulki biyo bayan sabon babban zaɓen ƙasar na shekarata2015.
An haifi Ibrahim Shema a ranar 22 ga watan Satumba a shekara ta 1957 a garin Dutsin-Ma da ke matsayin ƙaramar hukuma a jihar Katsina.
Ya halarci Makarantar Firamare ta Nasarawa, Katsina (1964-1971) da Makarantar Sakandaren Gwamnati, Kafanchan (1972-1976). Ya yi karatu a Kwalejin Arts, Science & Technology, Zariya daga shekara ta 1977 zuwa 1980, ya samu adimishan a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya kammala karatun digiri na biyu (LLB) a shekarar 1983. Bayan shekara ɗaya ya samu B.L a Nigerian Law School, Victoria Island, Lagos. A lokacin da yake aikin lauya, ya yi karatun digiri na biyu a fannin kasuwanci a Jami'ar Ahmadu Bello, inda ya kammala a shekarar 1998.
Ibrahim Shema ya kasance babban Lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari'a na jihar (Agusta 1999 - Mayu 2003) a lokacin da Umaru Musa Yar'adua ya ke a matsayin gwamnan jihar Katsina na farko. Daga nan kuma ya koma aikinsa na sirri a Kaduna. A watan Janairun shekarar 2005, an naɗa shi memba na kwamitin musamman na jam’iyyar PDP kan rikicin Anambra. Sannan ya riƙe muƙamin mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa ( shiyyar Arewa maso Yamma) (Satumba 2005 – Nuwamba 2006). A lokaci guda kuma, Ibrahim shema ya zama shugaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar PDP na ƙasa, kuma shugaban majalisar gudanarwa, Cibiyar Jam’iyyar PDPn.
Ibrahim Shema ya taɓa zama shugaban kwamitin sulhu na ƙasa na jam'iyyar PDP ta Kudu maso Kudu (Mayu zuwa Yuni 2006). Ya kuma riƙe mukamin Shugaban Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Najeriya (NAMA) daga watan Disamba shekarar ta 2005 zuwa Nuwamban shekarar 2006, a lokacin da ya lashe tikitin jam'iyyar PDP na tsayawa takarar gwamna a jihar Katsina a shekara ta 2007.
An zaɓi Ibrahim Shehu Shema a matsayin Gwamnan jihar Katsina a ranar 12 ga watan Afrilun shekara ta 2007, inda Ya gaji Marigayi Umaru Yar’adua mai barin mulki, wanda daga bisani shi kuma aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa. Ya hau karagar mulki ne a ranar 29 ga watan Mayun shekara ta 2007. An bayyana Shema a matsayin “gwamna mai rowa,” saboda kin buɗe rumfunan jihar Katsina ga ƴan siyasar Katsina, yanayin da yake da alaƙa da tsohon gwamnan jihar, Umaru Musa Yar'adua.
An sake zaɓen Ibrahim Shema na tsawon wasu shekaru huɗun a ranar 28 ga watan Afrilun shekara ta 2011, inda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP). Shema ya samu ƙuri’u miliyan ɗaya da dubu ashirin da bakwai da ɗari tara da sha biyu (1,027,912) sai Aminu Masari na jam’iyyar Congress for Progressive Change CPC, da ƙuri’u 555,769. Ɗan takarar jam'iyar Action Congress of Nigeria (ACN) ya zo na uku da kuri’u 19,990.
Wani jigo a jam’iyyar PDP a jihar Katsina, Tasiu Umar Mashi, ya rasu a watan Nuwamba shekarar 2009, a ofishin kwamishinan ƴan sandan jihar Katsina, Danazumi Doma. Taƙaddama game da lamarin da ya kai ga mutuwarsa ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin ɓangarorin PDP da ke adawa da Shema, ɗaya kuma ƙarƙashin jagorancin ministan noma da albarkatun ruwa, Dr. Abba Sayyadi Ruma. A watan Disambar shekara ta 2010, Shema ya sake lashe zaɓen fidda gwani na gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party, a fafatawar da shi kaɗai ne ɗan takara.
Ya auri Fatima Ibrahim Shema, su na da ƴaƴa huɗu, maza ukku (3) mace ɗaya (1), ya Kuma auri Maryam yar adua , yada da alhaji Kabir shema.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Ibrahim Shema, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.