Ahmad bin Ali Al-Hudhaify ɗaya ne daga cikin mahardata Alqur'ani mai girma kuma ɗaya daga cikin limamai da masu yin Khuɗuba a Masallacin Annabi Muhammad (S A W) da wasu Masallatan a ƙasar Saudiyya, ɗan liman kuma mai yin Khuɗuba a Masallacin ma'aiki (S A W).
Ali bin Abdul-Rahman Al-Huzaify, yana aiki a matsayin limami kuma mai Khuɗuba a Masallacin Annabi da ke Madina bayan ya kasance limami kuma mai Khuɗuba a masallacin Quba na Madina, kuma malami ne a jami’ar Taibah da ke Madina, kuma ya yi aiki a Jami'ar Musulunci da ke Madina, inda ya samu digiri na biyu da digirin digirgir inda ya fita da sakamako mai kyau sosai, wanda ya fita ne da first class, ya halarta majalisin karatuka da dama da laccoci da taron ƙarawa juna sani a ciki da wajen Madina.
Ahmad Aliyu Al-Huzaify | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a | |
Sana'a | qāriʾ (en) |
A cikin watan Ramadan na shekara ta, 1438, Babban Shugaban kwamiti mai kula da harkokin Masallacin Harami da Masallacin Manzon Allah (SAW) da ke Madina ta sanya Al- Hudhaifi ya jagoranci masu Al'ummar Musulmi a cikin Sallar Tarawihi a Masallacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, inda yaci gaba da gudanar da Jagorantar Sallah Tarawihi/Asham/Alkayeji a cikin watan Ramadan a shekarar, 1439 AH da 1440 AH. A shekara ta, 1441 bayan hijira, a ranar 13 ga watan Safar aka yanke shawarar nada shi a matsayin limamin masallacin Annabi a hukumance.
A cikin watan Disambar shekarar, 2022, an ba da izini don ya gabatar da Khuɗuba a Masallacin Annabi.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Ahmad Aliyu Al-Huzaify, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.