Yakubu Dogara CFR (an haife shi a ranar 26 ga watan Satumban shekara ta alif 1967).
Ya kasan ce ɗan Najeriya kuma ɗan siyasa, Ya kasance lauya yayinda daga bisani ya zama sipika a majalisar tarayyan Najeriya na goma sha hudu (14) daga shekara ta 2015-2019. Da farko Dogara ya kasance dan jam'iyyar PDP a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa ta Jihar Bauchi. Daga bisani ya koma jamiyyar All Progressives Congress (APC).
Yakubu Dogara | |||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 -
9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019
6 ga Yuni, 2015 -
6 ga Yuni, 2011 -
5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011 | |||||||||||
Rayuwa | |||||||||||
Haihuwa | 26 Disamba 1967 (56 shekaru) | ||||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||||
Karatu | |||||||||||
Makaranta | Jami'ar Jos | ||||||||||
Sana'a | |||||||||||
Sana'a | Lauya da ɗan siyasa | ||||||||||
Imani | |||||||||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party | ||||||||||
yakubudogara.com.ng |
An haifi Dogara daga ahalin Yakubu Ganawuri da Saratu Yakubu dogara a shekara ta alif 1967,ranar 26 ga watan Disamba.
Ya fara makarantar Firamare aji 6 a Gwarangah primary School a shekara ta alif 1976. A wancan karamar hukumar Tafawa Balewa na jihar Bauchi.
Dogara Yayi Makarantar Firamare Gwarangah Primary School, Tafawa Balewa L.G.A a jihar Bauchi. A Shekarar 1975. Daga bisani yayi Bauchi Teachers College a Shekarar 1982. Inda ya tafi jamiar Jos, Plateau State, inda ya samu digirinsa na lauya. A shekara ta alif 1992. Daga shekara ta alif 1992 zuwa 1993 yayi makarantar samun shaidan zama lauya a jihar legas.
An kirashi zuwa Bar a shekara ta alif 1993. Inda daga baya yayi mastas dinsa a Robert Gordon University Aberdeen Scotland.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Yakubu Dogara, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.