Tsamiya: Itaciyar Bishiya ce da ake samu a Afirka

Tsamiya bishiya ce mai amfani sosai.

Bincike ya tabbatar da cewa dukkanin jikin bishiyar tsamiya yana da amfani (Masset, Candia da Ocheng, 2015; Gilma da Watson, 1994; Muzaffar da Kumar, 2017), wanda ka iya zama amfanin abinci, magani, kayan aiki kamar katako ko makamashin wuta.

Tsamiya
Tsamiya: Asali, Sunayen Tsamiya a wasu yarukan, Wuraren da aka fi samun tsamiya
Conservation status
Tsamiya: Asali, Sunayen Tsamiya a wasu yarukan, Wuraren da aka fi samun tsamiya
Least Concern (en) Fassara (IUCN 3.1)
Scientific classification
KingdomPlantae
OrderFabales (en) Fabales
DangiFabaceae (en) Fabaceae
TribeAmherstieae (en) Amherstieae
GenusTamarindus (en) Tamarindus
jinsi Tamarindus indica
Linnaeus, 1753
General information
Tsatso Tamarind seed oil (en) Fassara, tsamiya da tamarind (en) Fassara
Tsamiya: Asali, Sunayen Tsamiya a wasu yarukan, Wuraren da aka fi samun tsamiya
Tsamiya: Asali, Sunayen Tsamiya a wasu yarukan, Wuraren da aka fi samun tsamiya
ganyen tsamiya
Tsamiya: Asali, Sunayen Tsamiya a wasu yarukan, Wuraren da aka fi samun tsamiya
furen tsamiya
Tsamiya: Asali, Sunayen Tsamiya a wasu yarukan, Wuraren da aka fi samun tsamiya
itacen tsamiya

Asali

Bishiyar tsamiya 'yar asalin Yammacin Afirka ce (Muzzafar da Kumar, 2017;

Massete, Canadia da Ocheng, 2015).

Sunayen Tsamiya a wasu yarukan

Asalin sunan tsamiya a kimiyyance shi ne Tamarindus Indica L. A Turance kuma sunanta Tamarind. Larabawa kuma suna kiranta da Tamri hindi ( ﺗَﻤﺮِ ﻫِﻨﺪِﻯ ).

Wuraren da aka fi samun tsamiya

Tsamiya, bishiya ce wacce take iya rayuwa a cikin zafin hamada mai tsanani, matsakaici da ma guraren da basu da zafin. Guri guda da tsamiya ba ta iya rayuwa a gurin shi ne guri mai gishiri. Wannan dalilin ne ya sa bata iya rayuwa a bakin teku saboda haka ta zamo bishiyar daji amma bata cika rayuwa a cikin kurmi ba. Amma duk da haka akwai ƙasashen da ake yin gonarta a reneta don amfanin jama'a.

Sassan Jikin Tsamiya

  1. Saiwa: Ana amfani da saiwar tsamiya wajen haɗa magungunan gargajiya.
  2. Gangan Jiki: Shi ne abin da ya fito daga ƙasa har zuwa rassa, abin da za a iya kira itace ko iccen tsamiya. Ana amfani da shi wajen yin katako domin gini. Rassan kuma ana rufin ɗaki da su. An tabbatar da cewa gara bata cin katakon da aka yi daga itacen tsamiya. Sannan kuma ana yin makamashin wuta da itacen tsamiya, kai tsaye ko kuma ta hanyar yin gawayinsa, kuma gawayin itacen tsamiya yana jimawa yana ci (ba kamar sauran ba da suke ƙonewa dawwuri).
  3. Ganye: Ana amfani da ganyen tsamiya a matsayin abincin dabbobi. Sannan kuma ana haɗa magani da ganyen tsamiya a kimiyyance da kuma gargajiyance.
  4. 'Ya'yan Tsamiya: Shi ne sashe mafi muhimmanci a jikin tsamiya. Domin a same shi ake shuka ta. Dukkan amfaninkan tsamiya da kuma sinadaran da ake samu a jikin tsamiya da za a zayyano a ƙasa a kansu za a yi magana.
  5. Kwanson ‘Ya’yan Tsamiya: Ana amfani da shi wajen haɗa magani.
  6. Ƙullon Tsamiya: A cikin ‘ya’yan tsamiya idan aka cire kwanson, aka fito da asalin ‘ya’yan, suma a cikinsu akwai ƙullo; wato irin tsamiyar kenan. Da shi ake sake samar da wata tsamiyar. Sannan kuma a kimiyyance ana yin roba da su sannan kuma akwai wani sinadari da ake kira fektin (Pectin) wanda ake saka shi a cikin magani domin ya bai wa magani kariya daga lalacewa.
  7. Fure: Ana kiwon zuma da furen tsamiya saboda tana matuƙar son ƙamshin. Sannan kuma dai ana haɗa magani da shi.
  8. Tsoka: Tsokar ‘ya’yan tsamiya ana amfani da ita a gargajiyance wajen fitar da tsatsa daga jikin abubuwan da suka haɗa da zinare, azurfa, tagulla da sauransu.

Kiwon Lafiya

Amfanin tsamiya a ɓangaren abin da ya

shafi kiwon lafiya ya haɗa da:

  • Narkar da abinci.
  • Saka jiki hutu.
  • Ƙarin jini.
  • Saukar da gudn jini, kasantuwar tana ɗauke da sinadarin fotashiyom. Wannan sinadari kuma zai taimaka wa masu hawan jini wajen rage wa jinin gudu har ya hana shi hawa. Sannan kuma wanda ba shi da wannan larura to zai samu kariya daga hawan jini.
  • Taimaka wa jijiya ta yi aiki. Sinadarin siyamin (Thiamin) da yake a cikin tsamiya shi yake taimaka wa jijiya ta yi aikin da ya dace a cikin jikin ɗan’adam.

Manazarta

Tags:

Tsamiya AsaliTsamiya Sunayen a wasu yarukanTsamiya Wuraren da aka fi samun tsamiyaTsamiya Sassan Jikin Tsamiya Kiwon LafiyaTsamiya ManazartaTsamiya

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

RaƙumiAbraham Ossei AidoohHarshen HausaLandanSadiya GyaleRafiu Adebayo IbrahimBashir Aliyu UmarMurtala MohammedMuhammadu Kabir UsmanAzareImam Al-Shafi'iBukin Suna a al'ummar HausawaJa'afar Mahmud AdamThe emily man fimPharaohYusuf Maitama SuleMacijiJamila NaguduGhanaOmkar Prasad BaidyaIbrahim BabangidaAl'adaRahama hassanSallar Idi BabbaGidan zooIbn TaymiyyahIbrahim DaboJapanSalatul FatihKayan aikiBangladeshIyaliJemageAhmadu BelloSaddam HusseinHabaiciOmanLilin BabaMaƙeraBayanauKofi AnnanKairoMaryam BoothMoscowJigawaDahiru MohammedAbba el mustaphaJerin ƙasashen AfirkaBindigaShukaTumfafiyaOkafor's LawCristiano RonaldoMaiduguriRahma MKFalasdinuZumunciBiyafaraGabonFasahaGafiyaHaboƘofofin ƙasar HausaBabba da jakaYahudawaMessiIngilaGinen EkweitaMuhammad Ibn Musa AlkhwarizmiNana Asma'uShruti HaasanMohammed WakilMal Samaila SuleimanKimiyyar zamantakewa🡆 More