Sha'aban Ibrahim Sharada (an haife shi ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1982), ɗan siyasan Najeriya ne kuma ɗan jarida daga jihar Kano wanda ya kasance mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa Muhammad Buhari kafin ya zama ɗan majalisar wakilai a shekara ta 2019.
Sha'aban Ibrahim Sharada | |||
---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Kano, 1 ga Janairu, 1982 (42 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
An haifi Sha'aban ne a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1982 a unguwar Sharada da ke karamar hukumar Kano, ya halarci makarantar firamare ta Salamta, sannan ya halarci Sakandaren Gwamnati na Sharada. Ya yi Digirin sa na farko a fannin (Mass Communication) a Jami'ar Bayero, Kano.
Sha'aban Sharada ya fara aiki ne a matsayin mataimaki na kasuwanci a Freedom Radio Nigeria da ke jihar Kano har zuwa lokacin da ya zama mataimaki na musamman ga shugaban tarayyar Najeriya Muhammad Buhari.
Sha'aban ya fara harkar siyasa ne a shekarar 2009 a lokacin da yake karatun digiri na farko inda ya tsaya takarar Sakataren yada Labarai na Kungiyar Dalibai ta kasa ta kasa reshen Jihar Kano kuma ya fara nada shi a matsayin Mataimaki na Musamman ga Shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari. A shekarar 2016, an zabi Sha'aban mamba a babban zaben Najeriya na 2019 don wakiltar Kano Municipal Constituency a majalisar wakilai ta Najeriya.
A halin yanzu shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilai kan tsaro da leken asiri.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Sha'aban Ibrahim Sharada, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.