Sana'o'in Hausawa Na Gargajiya

Sana'o'in Hausawa na gargajiya na nufin sana'o'in asali na mutanen Hausa na farko wanda aka san su da shi.

Wadannan sana'oi sun kasance tushen tattalin arzikin kasashen Hausa tun a farkon, tarihinsu. Daga ciki akwai noma da rini da jima da kira da dai sauransu.

Sana'a

Sana’a kalma ce da aka aro ta daga Larabci, kuma tana ɗaukar ma’ana ta samar da wani abin amfani ta hanyar hikima a Hausance. Misali, sana’ar ƙira. A gargajiyance, Bahaushe yana da sana’o’in da yawansu ke da wahalar ƙididdigewa. Daga cikin irin waɗannan sana’o’i akwai manya, akwai kuma ƙanana, akwai na maza, akwai kuma na mata, sannan kuma akwai na gama-gari. Sannan kuma masana sun kasa su zuwa kashi uku wadanda suka haɗa da sana’o’in maza da na sana’o’in mata da kuma sana’o’in haɗaka ko na gamayya.

Sana'a na nufin duk wani nema ko hanyar da Dan Adam zai nemi abinci ta hanyar halak, ko kuma sana'a ita ce duk abinda mutun zai sarrafa domin ya sami wata lada, ya samu ya rayu, rayuwa mai kyau ba tare da wani cikas ba. Ko kuma a takaice mu ce sana'a na nufin dogaro da kai. Sana'ar mutum ita ce a bar alfaharinsa ko ina ya je da ita zai tinkaho. Akwai wasu mawakan Hausa da dama da suka y0i tsokaci a kan Sana'a, har wata daga cikinsu tana cewa a lokacin da take zaburar da mata a kan sana'a "Kai ku tashi ku koyi sana'a mata, macen da ba ta sana'a aura ce" kalmar aura a nan tana nufin jaka.

Sana’o’in maza su ne sana’o’in da maza zalla ne suka fi yin su. Koda an samu mata a ciki to yawansu bai kai a misalta ba. Misali, sana’ar ƙira da sauransu. Ire- Iren wadannan sanao’in gargajiya na Hausawa sun hada da:

  1. Noma
  2. saƙa
  3. Fawa
  4. Sassaka
  5. Sussuka
  6. Fatauci
  7. Su(Kamun kifi)
  8. Dukanci
  9. Wanzanci
  10. Kiwo
  11. Rini
  12. Jima
  13. Ƙira
  14. Farauta
  15. Kasuwanci

Bayanin su

Bayan mun ga Ire-iren su bari mu tafi zuwa bayaninsu daya

bayan daya da kuma abubuwan da suka kunsa.

Noma

"Noma na duke tsohon ciniki shine kirarin noma da Hausawa suke masa da dadewa". A ƙasar hausa dacan babu wata babbar sana’a wadda zance maka kusan kowa yana yinta da ta wuce noma. Inda mafi yawancin Kakanni suke amfani da noma domin cida iyalansu ta hanyar shuka abun da zasu ci da kuma saidawa. Shi noma ya kasu ne zuwa gida biyu ga su kamar haka:

  1. Noma domin cida gida: Mafi yawancin noman da hausawa suke yi a ƙasar hausa a dacan sukeyi musamman talakawan da wanda zasu cida iyalinsu kawai, wanda zaka ga mutum ya noma abunda zasu ci da iyalinsa kawai. Misalin irin wannan shine wanda yake shuka hatsi irinsu masara, dawa, gero da ma sauransu waɗanda ake sarrafawa zuwa abincin gargajiya.
  2. Noman Kasuwanci: Nau’i na biyu kuma shine wanda domin sai dawa kaɗai ake yinsa wanda ba a iya ci ya tsaya ba kamar waɗanda suke noma shukoki irin auduga da kuma irinsu ridi da sauransu. Duk da cewa daga baya an runguma noman Masara da Shinkafa da sauransu a matsayin noman kasuwanci.

Kiwo

Kiwo dai itace babbar sana'ar Fulani kuma sunfi kowace Ƙabila iya kiwo da yawan dabbobi, kamar yadda Noma yake babbar sana'ar Hausawa haka suma Fulani kiwo shine babbar sana'ar su. Sai dai kuma Kiwo na daga cikin sana’oi wanda suka shahara a wajen hausawa wanda suke yi tun kaka da kakanni. Hausawa sun daɗe suna kiwata dabbobi daban-daban kama tun daga mayan dabbobi zuwa ƙananan dabbobi. Misalan wasu daga cikin dabbobin da hausawa suka daɗe suna kiwatawa sun haɗa da kaza, fannin raguna, shanu rakuma da sauransu. Yawancin dalilin da yake sa ana kiwo shine domin a sai da a samu kuɗi don biyan wasu buƙatun yau-da-kullum, wani lokacin kuma domin a yi aikin noma da su Misali shanun Noma (Ga'in huɗa).

Rini

Sana’ar hannu ce wadda ake yi, yadda take shine ana canza

ma kaya launi ko kuma kala ta hanyar rina su da sinadarai.

Da dadewa hausawa sun dade suna rina kayansu wanda

wadanda ke rini a hausa ana kiransu da marina.

Dalilin yinsa shine don a samu kudi da wanda rini har yanzu

ana yinsa a yankunan hausawa daban daban a fadin duniya.

Jima

Tunda daɗewa an daɗe duniya ana jima bama a ƙasar hausa kawai ba, inda ake saida abubuwan da ake haɗa sanadiyyar jima a kasuwa. Jima tana nufin samun fata ta dabbobi a tsaftace ta yadda za’a sarrafa ta zuwa abubuwan amfani. Misalin abubuwan da ake haɗawa daga jima sun haɗa da sulke, takalma, buzu da saurandsu.

DUKANCI

Sana’ar Dukanci, sana’a ce da ake sarrafa fata a mayar da ita wani abu mai amfani

kamar takalmi, guga, riga da sauransu domin samun abin masarufi. Baduku shi

ne sunan mai yin sana’ar Dukanci. Fatar da masu jima ke samarwa, ita dukawa

ke sarrafawa. Akwai unguwar da ta yi fice a kan wannan sana’a a cikin birnin

Kano da ake kira Dukawa.

-Kayan Aiki

Dukawa sukan gudanar da sana’arsu ta

dukanci ta hanyar amfani da kayayyakin da suka haɗa da: fata, almakashi,

guduma, da sauransu

-Kayayyakin da Dukawa ke Yi

Matashi (fulo), majingini, buzu, laya, guru, daga, kambu, salka, garkuwa,

maratayi, taraha/tintimi, rigar sirdi, ragama, kube, gafaka, zabira, linzami,

takalmi, kwari, tandu, burgami, warki, guga, dagumi, sulkami, zugazugi (abin da

masu sana'ar ƙira ke hura wuta da shi), taiki, da sauransu.

KIRA

Ko shakka babu kira na daya daga cikin sanaoin gargajiya na

hausawa wanda suke yi tun zamanin kaka da kakanni.

Yadda ake kira shine za’a samu karfe a sa shi cikin wuta yayi

ja yadda za’a sarrafa shi zuwa abubuwan amfani.

Wanda yake kira ana kiranshi da makeri shikuma wajen da ake

kirar ana kiranta da makera.

Misalan abubuwan da ake kerawa sun hada da abubuwan aikin

gona akamar su lauje, hauya, gatari, mijagara da sauransu.

Akwai kuma abuwan yaki wanda suma a makera ake hada su

kamar su Takobi, adda, makari mashi, kibiya da sauransu.

FARAUTA

Farauta na nufin kamo dabbobin daji ta hanyar halbo su ko

kuma yi masu tarko yadda za’a kamasu.

Farauta ana yinta ne musamman don kamo nama daga daji

domin a ci ko kuma a sai da a kasuwa ga wanda suka dauke

ta a matsayin kasuwanci.

Wanda ya dauki farauta a matsayin kasuwanci ana kiranshi da

mafarauci a kasar hausa.

Sana'a

GA JERIN SANA'O'IN HAUSAWA

1. 'Kafinta shi Kafinta kala biyu ne akwai na sama akwai kuma na kasa, Kafinta sama shine wanda yake bugun kwano wato rafta da dai sauran su. Shi kuma Kafinta kasa shine mai hada kujeru da gadaje ds.

2. Su/Masunci/Mai kamun kifi Su sana'a ce mai zaman kanta wadda itama akan dogara da ita, tunda zaka ga da yawa masu yin su har bada maganin sanyi suke saboda alakar su da ruwa. Su na daga sana'a da ake gado tun daga iyaye har kakanni.

3. Qira Qira ita sana'a ce mai zaman kanta wadda itama akan dogara da ita wato qira na nufin sana'a ce da ake sanin yadda ake sarrafa karfe da wuta. Itama akan gade ta iyaye da kakanni masu qira na bada maganin wuta. 4. Kiɗa kida itama sana'a ce da akanyi ta a kasar Hausa tun zamanin da, itama akan dogara da ita. Makada sun kasu daban daban akwai makadin noma, na fada, na yan'bori da kuma makadi game gari shi kam kowa yana wa kids sarki, yan'bori manoma ds.

5. Sassaka itama sana'a ce da mai zaman kanta wadda masassaka keyin ta misali suna sassaka turmi tabarya, Kota/fartanya ds.

6. Dukanci ita dai sana'a baduku sana'a ce ta sanin yadda ake sarrafa fata da irin guru da layun nan gargajiya wato masu dinka laya.

7. Wanzanci itama sana'a wanzaci sana'a wadda Hausawa keyin ta misali sune sukeyin aski, kaciya ds.

8. Dinki' sana'a dinki sana'a ce da akeyi don dogaro da kai madunka suna dunka riguna sawa na maza da mata iri daban daban.

9. Noma shima noma sana'a ce mai mutukar amfani wadda itama da itace wasu suka dogara.

10. Kiwo sana'a kiwo sana'a ce wadda fulani suka fi shahara a cikin ta, tunba kiwon shanu ba, kusan dukan Annabawa sunyi kiwo.

11. Kasuwanci/Fatauci kasuwanci sana'a ce wadda ta samo asali tun daga fiyayyen halittu (S A W) yayin da itace sana'a da aka fi shahara akanta kusan acikin ko wace Al-ummah.

12. Gina/Gini Gina itama ta kasu kashi biyu akwai masu ginin gidaje sai kuma masu ginin tukwane ds.

13. Ɗori itama sana'a ce da mafi yawan ta gadon ta ake daga iyaye da kakanni. Wato madora sune masu dora mutum idan ya karye har ma dabbobi. Da dai sauran sana'o'in Hausawa da bamu ambata ba. Wadannan sune a takaice. Amma akwaisu da yawa bazasu ƙirgu ba.

Sana'o'in Mata

Suma dai matan Hausawa ba'a barsu a baya ba domin kuwa tun zamanin da suna yin sana'a ballantana wannan zamani

1. 'Kitso' sana'ar Kitso sana'a ce da mata sukeyin ta domin samun yan kwabbai kuma domin su taimaka ma junansu. wasu tun suna yara suke koyo wasu kuma sai sun girma. Amma yanzu sukan bude saloon na zamani.

2. Fura itama sana'a ce ta Mata wadda akeyin ta don sai fura wani lokacin ma hada Nono.

3. Tuwo itama sana'a ce ta saida tuwo wadda aka fi sani da tuwo-tuwo, mafi yawa Mata keyin ta.

4. Kaɗi kaɗi sana'a ce ta Mata wato masu sarrafa Auduga/kaɗa don yin wasu abubuwa tunba mazari da kuma kayan sawa. Amma yanzu ba'a yi sana'a ta koma ta zamani.

5. Koda itama sana'a ce da mata keyi musamman tsofaffi, sana'a Koda na nufin sussukau mata masu sussukau hatsi musamman gero dawa ds. Amma anfi yin wannan sana'a a kauyuka. Yanzu ma dai ta kusa komawa ta zamani da inji akeyin sussuka.

6. Lalle/kwalliya itama sana'a ce wadda Mata keyi musamman idan za'a kai sabuwa amarya. Wato lallen Amare.

7. 'Reda' Reda sana'a ce da mata keyi amma a da can lokacin da babu wadatuwar injina musamman kauye. Anayin reda ne wata Nika hatsi masara,dawa, gero da dai sauran su don yin tuwo. Duwatsu ne guda biyu daya sama daya kasa sai adinga zuba hatsi ana gogawa har ya zamo gari.

Amfanin Sana'a

Sana'a tana da amfani sosai don akasar Hausa idan mutum baida sana'a ko aure ba'a bashi babban amfani sana'a tana sa a samu Al-ummah managarciya watau ingantacciya.

Manazarta

Tags:

Sana'o'in Hausawa Na Gargajiya SanaaSana'o'in Hausawa Na Gargajiya Bayanin suSana'o'in Hausawa Na Gargajiya NomaSana'o'in Hausawa Na Gargajiya KiwoSana'o'in Hausawa Na Gargajiya RiniSana'o'in Hausawa Na Gargajiya JimaSana'o'in Hausawa Na Gargajiya DUKANCISana'o'in Hausawa Na Gargajiya KIRASana'o'in Hausawa Na Gargajiya FARAUTASana'o'in Hausawa Na Gargajiya Amfanin SanaaSana'o'in Hausawa Na Gargajiya ManazartaSana'o'in Hausawa Na GargajiyaHausa BakwaiHausawa

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Shi'a a NajeriyaJerin ƙauyuka a jihar KanoRukuninAbba Kabir YusufAnnabi IsahMansur Ibrahim SokotoShehu Hassan KanoYemenAlqur'ani mai girmaJerin Gwamnonin Jahar SokotoHamisu BreakerZinareBukukuwan hausawa da rabe-rabensuMala`ikuAlhasan ɗan AliSan FranciscoDikko Umaru RaddaMuhammad Ibn Musa AlkhwarizmiGaisuwaGyaraBauchi (birni)KroatiyaIbrahim ZakzakyMaitatsineTarihiAshiru NagomaAminu Ibrahim DaurawaMurja IbrahimManyan Fina-finan Masar 100 na Bibliotheca AlexandrinaKainuwaJerin ƙauyuka a jihar KadunaBagaruwaWikiquoteYaran AnnabiJoseph Nanven GarbaIsrai da Mi'rajiMarsha CoxItofiyaIsah Ali Ibrahim PantamiKasuwaElizabeth TaylorJerin Sunayen 'yan majalisar wakilan Najeriya, 2019–2023AntatikaKhalid ibn al-Walid2021Sahabban AnnabiTsohon CarthageKoriya ta KuduHaɗejiyaAmurka ta ArewaMakarantar FiramareRyan de VilliersJerin shugabannin ƙasar NijarAlhassan DantataOncologyHannatu BashirAhmad Mai DeribeMisraMarisTehranMarsAljeriyaHadiza AliyuAbay SitiMuhammadKhulafa'hur-RashidunNahawuAdamawaMartha AnkomahNuhuKogin LogoneBet9jaMorocco🡆 More