Madara ko Nono dukkanin kalmomin biyu suna nufin abu ɗaya ne sai dai akan banbanta halittar mama ta Ɗan Adam a kirata da Kalmar Nono kawai ba'a kiranta da madara.
Idan aka ce Nono to ana nufin ruwan dake fita daga nonuwan halitta walau ta Ɗan Adam ko ta Dabba misali mace tana fitar da nono a sanda ta haihu Dan shayar da jaririnta, haka kuma dabbobi kamar saniya, tunkiya, akuya, suma suna fitar da nono dan shayarwa, sa'annan idan kuma aka ce Madara to anan ana nufin nono ne wanda aka samosa ba daga jikin halitta ba amma dai ansa mesa ne daga wasu nau'ukan bishiyoyi, tsirrai, ko kayan abinci, kamar kwa-kwa, waken-suya, gyaɗa, dadai sauransu. Madara ko Nono dai wani farin ruwa ne dake ɗauke da sinadarai masu amfani a jikin dan Adam, madara dai ta kasance ita kaɗai ce ake amfani da ita domin samarwa jarirai abinci na ɗan Adam ko dabba kafin su kuma iya fara cin abinci, nono na dauke da wasu kwayoyin halittu dake fita daga jikin uwa zuwa jikin jariri dan su kareshi daga cututtukan da zasu iya samun jaririn, wannan yasa uwa ta shayar da jaririnta abu ne mafi mahimmanci a rayuwar jariri.
Madara | |
---|---|
abinci, food ingredient (en) , body fluid (en) , emulsion (en) , secretion (en) , particular anatomical entity (en) , dairy-milk beverage (en) da non-alcoholic beverage (en) | |
Kayan haɗi | liquid water (en) , protein (en) , fat (en) da sodium chloride (en) |
Tarihi | |
Mai tsarawa | mammal (en) |
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Madara, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.