Jelani Aliyu: Maizanen mota a Najeriya

Jelani Aliyu (akuma n haife shi a ranar 11 ga watan Satumban Shekarar 1966) ɗan Najeriya ne mai ƙera motoci, wanda ya yi aiki da kamfanin ƙera motoci na Amurka General Motors.

Ya kasance babban mai tsara zane-zane a GM, har zuwa lokacin da shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa shi a matsayin Babban Darakta na Hukumar ƙera motoci da cigaban Najeriya (NADDC) a shekarar 2017.

Jelani Aliyu: Tasowa da Ilimi, Aiki, Sanannun Zayyanoni Jelani Aliyu
Jelani Aliyu: Tasowa da Ilimi, Aiki, Sanannun Zayyanoni
Rayuwa
Haihuwa Kaduna, 11 Satumba 1968 (55 shekaru)
Karatu
Makaranta College for Creative Studies (en) Fassara
Sana'a
Sana'a designer (en) Fassara da ɗan kasuwa
jelanialiyu.com
Jelani Aliyu: Tasowa da Ilimi, Aiki, Sanannun Zayyanoni
Chevrolet Volt ɗaya daga cikin motar da Jelani Aliyu ya zana
Jelani Aliyu: Tasowa da Ilimi, Aiki, Sanannun Zayyanoni
Chevrolet Volt, ɗaya daga cikin motar da Jelani Aliyu ya zana

Tasowa da Ilimi

An kuma haifi Aliyu a shekarar 1966 a Kaduna Nijeriya, a cikin dangin Alhaji Aliyu Haidar da Hajiya Sharifiyya Hauwa Aliyu, shi ne na biyar a cikin ’ya’ya bakwai a gidan wadanda ’yan asalin Dogon-daji ne a Jihar Sokoto , wannan ne ya sa aka koma da matashin Aliyu Sokoto don neman ilimi. Ya yi karatu a Sokoto Capital School daga shekarar 1971 zuwa 1978 sannan ya yi karatu a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Sakkwato inda ya samu lambar yabo na dalibin da ya fi kowa yaye a Technical Drawing.

A shekarar 1986, Aliyu ya sami admission don karantar Architecture a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria. Sai dai da sauri Aliyu ya fice daga jami'ar inda ya gano cewa karatu a jami'ar da wuya ya ba shi damar ci gaba da burinsa na zama mai zanen mota domin karatu a can baya aiki kamar yadda ake yi a polytechnic sannan ya wuce zuwa Federal Polytechnic Birnin Kebbi da ke Kebbi State daga 1986 zuwa 1988 inda ya sami associate digiri a fannin architecture tare dkuma a lambar yabo na Gwarzon Ɗalibai. Yayin da yake can ya fara neman izinin shiga makarantun zane a Turai da Amurka wanda zai kai shi GA sana'ar Ƙera motoci.

A shekarar 1990, Hukumar bayar da tallafin karatu ta Jihar Sakkwato ta dauki nauyin daukar nauyin Aliyu don yin karatu a Amurka a College for Creative Studies da ke Detroit don karantar fasahar kere-kere. Yayin karatun Aliyu ya sami lambobin yabo biyu masu daraja daga Kamfanin Motoci na Ford da Michelin, Amurka. A shekarar 1994, Aliyu ya samu digirin sa a fannin kera motoci, nan take ya shiga tawagar [General Motors], inda ya fara aikin ƙere-ƙere.

Aiki

A shekarar 1994 bayan kammala karatunsa daga College for Creative Studies, Aliyu ya shiga General Motors. A General Motors Aliyu shi ne mai co-desinger na Oldsmobile Bravada, [[Buick]. Rendezvous]] da Opel Astra kuma shine jagorar zanen waje na Pontiac G6 da Chevrolet Volt, abin hawa na lantarki tare da sleek arcing roofline.

Lokacin da yake magana game da inspiration na sana'arsa ta ƙera motoci a cikin wata hira, Jelani ya ce;

Na kasance ina son zane. Waɗannan abubuwa ne daban-daban a kusa da ni, mutane, abubuwa, tsire-tsire, da kuma abubuwa daga tunanina. Na girma cikin ƙaunar science fiction sannan kuma a cikin fina-finai, za ku ga yawancin spacecraft na zayayyu da sauran abubuwa na futuristic waɗanda za su ƙarfafa ni in yi hangen nesa. Ina kuma son motoci sosai, duk da cewa a lokacin ba mu da Ferrari a Sakkwato. Duk da haka, muna da mujallu da na gan su, kuma sun ƙarfafa ni. Don haka na haɗa soyayyata na zane da motoci na yanke shawarar zama mai zanen mota.

Ya kuma ce, abin da ya zaburar da shi iyayensa ne domin sun bar shi ya yanke shawarar abin da yake son yi. Misali, lokacin da ya je Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya yanke shawarar ba zai ci gaba da zama a can ba, sun ƙarfafa masa guiwa. Ba su nace cewa dole ne ya zauna a wurin ba. Akan zanen Chevrolet Volt, ya ce;

Duba wani ɗan ƙaramin ganye, kauri ne kawai na 'yar millimita amma duk da haka ingantacciyar masana'anta ce,.. Na yi ƙoƙarin fahimtar ingancin yanayi da ƙirarsa kuma na jawo waɗannan concepts na yi amfani da su a Chevrolet Volt.

Sanannun Zayyanoni

  • 2004 Pontiac G6
    Jelani Aliyu: Tasowa da Ilimi, Aiki, Sanannun Zayyanoni 
    Pontiac G6 GT Street Edition Convertible (Orange Julep)
  • 2010 Chevrolet Volt
Jelani Aliyu: Tasowa da Ilimi, Aiki, Sanannun Zayyanoni 
President Barack Obama behind the wheel of a new Chevy Volt during his tour of the General Motors Auto Plant in Hamtramck, Michigan

Kuma ga

  • Chuck Jordan (automobile designer)
  • Strother McMinn
  • Helene Rother

Manazarta

Haɗin waje

Template:Gm designers

Tags:

Jelani Aliyu Tasowa da IlimiJelani Aliyu AikiJelani Aliyu Sanannun ZayyanoniJelani Aliyu Kuma gaJelani Aliyu ManazartaJelani Aliyu Haɗin wajeJelani AliyuAmurkaMuhammadu BuhariNijeriya

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

ƘaranbauMalam Lawal KalarawiNew YorkBirnin LuxembourgDubai (birni)Abubakar ImamIndustrial RevolutionCyrus the GreatIyaliGwamnatiBayajiddaAisha Musa Ahmad (mawakiya)Tantabara1991BayelsaJapanBeljikJerin ƙauyuka a Jihar GombeFati WashaMalam MadoriMansa MusaJinin HaidaYusuf Baban CineduUlul-azmiGoogleJoseph Nanven GarbaEbrahim RaisiSeptember 11 attacksMaryam BoothAl-GhazaliAlbarkatun dan'adamCibiyar DanquahMuhammadu BelloDahiru Usman BauchiKameruMutuwaƘur'aniyyaMaiduguriAbubakarIspaniyaHispaniaTuranciGaisuwaJimlaDutsen ArfaMala`ikuMorokoBabban shafiAskiMahmood shahatRed SeaLarabciJamhuriyar KwangoShehu Musa Yar'AduaJahar TarabaGabasHamza al-MustaphaAsalin wasar Fulani da BarebariKanawaJamila NaguduJamhuriyar Najeriya ta farkoCutar AsthmaYahaya AbdulkarimSallar GaniKimiyyaShuaibu KuluTanzaniyaKabewaZenith BankYakubu GowonWasan kwaikwayoAmina J. MohammedBilkisuSin🡆 More