Aminu Ado Bayero An haife shi ne a shekera ta alif dari tara da sittin da ɗaya (1961), shi ne Sarkin Kano na (15), daga ƙabilan Fulani na Sullubawa.
Ya hau kan karagar mulki ne a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2020, bayan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya sauke sarki Muhammad Sanusi II daga kan karagar mulkin sarautar Kano. shine Chancellor na jami'ar calabar
Aminu Ado Bayero | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kano, 1961 (62/63 shekaru) |
ƙasa | Kano |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Ado Bayero |
Ahali | Nasiru Ado Bayero |
Karatu | |
Makaranta | Government College, Birnin Kudu Jami'ar Bayero |
Harsuna | Turanci Hausa |
Sana'a | |
Sana'a | Emir (en) |
Aminu Ado Bayero ya fito ne daga jihar Kano, kuma shi ne na biyu a cikin 'ya'yan Ado Bayero, wato Sarkin kano na (13). Aminu Ado ya halarci makarantar firamare ta ƙofar Kudu sannan ya wuce zuwa makarantar sakandare ta Gwamnati, Birnin Kudu. Aminu Ado ya karanci fannin sadarwa mai yawa daga Jami’ar Bayero Kano, sannan kuma ya tafi Kwalejin Flying, dake Oakland, California, a Amurka, kafin yaci gaba da shiga Ofishin Kula da Matasa na Kasa a Hukumar Gidan Talabijin ta Najeriya, Makurdi.
Aminu Ado ya yi aiki a matsayin jami’in hulda da jama’a a kamfanin jirgin Kabo, kafin ya zama injiniyan jirgin sama. A shekara ta (1990), mahaifinsa, Ado Bayero ya naɗa shi Ɗan Majen Kano kuma shugaban gundumar Dala tun kafin ya kara daukaka shi ga Ɗan Buram ɗin Kano a watan Oktoba na wannan shekarar. A shekara ta (1992) , an inganta shi zuwa Turakin Kano da kuma Sarkin Dawakin Tsakar Gida Kano a shekara ta (2000). Ya kuma yi aiki a matsayin shugaban kwamatin masarautar Kano. A shekara ta ( 2014) , mai martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya daukaka shi zuwa Wamban Kano, don haka ya canza shi daga Dala zuwa karamar hukumar Birni da kewaye, inda ya maye gurbin Galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim a matsayin shugaban gundumar.
A shekara ta (2019), gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya naɗa shi a matsayin Sarkin Bichi.
A ranar (9), ga watan Maris shekara ta (2020), an nada shi a matsayin sarki na (15), na jihar Kano, don maye gurbin Muhammad Sanusi II, wanda aka hambarar dashi a wannan ranar.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Aminu Ado Bayero, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.