Amina Titi Atiku Abubakar

Amina Titi Atiku Abubakar ta kasance ɗaya daga cikin matan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar.

Tana daga cikin masu assasa 'yancin yara, kuma ita ta samar da ƙungiyar kula da satan yara da mata wato Gidauniyar Masu Fataucin Mata da Kawar da Aikin yi da Yara (WOTCLEF) kuma tana daga cikin waɗanda suka assassa kafa hukumar kula sace-sacen yara na mata na Hukumar hana fataucin Bil-Adama ta Ƙasa (NAPTIP).

Amina Titi Atiku Abubakar Amina Titi Atiku Abubakar
Rayuwa
Haihuwa Osun, 6 ga Yuni, 1949 (74 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Ƴan uwa
Abokiyar zama Atiku Abubakar
Karatu
Makaranta Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a gwagwarmaya da ɗan siyasa

Kuruciya da Ilimi

An haifi Titi Abubakar a iyalan yarbawa daga ilesa na jihar Osun. Tayi ilimin firamare a makarantan Lafiaji, Lagos sannan kuma ta cigaba da karatun ta na sakandire a makarantar St. Mary's Iwo, har zuwa shekara ta 1969i a jihar Lagos.

Ta auri Atiku Abubakar a lokacin yana jami'in Custom kafin daga baya ta halarci Kaduna Polytechnic. Bayan turanci, Titi tana jin yarukan yarbanci da kuma hausa sosai. Ta karbi addinin musulunci daga bisani.

Aiki

Ta kasance malama a kwalejin fasaha ta jihar kaduna.

Bayan ta cigaba da karatun ta a shekara ta 1986 zuwa shekarar 1987 a kasar Roma, ta hadu da yan matan Nigeria da yawa sun wanda ke sana'ar karuwanci ga uwargoyoyinsu, kuma galibi ba biyansyu akeyi ba. Kuma ta gano galibi an yaudare su ne da cewa zsuyi aiki a kasar italiya ko wasu kasashen ketare. Sannan kuma ta ci alwashin yaki da wannan rashin adalcin.

WOTCLEF & NAPTIP

Wannan ne yasa titi tayi alkawari domin magance wannan matsalan da suka faru bayan dawowar ta a shekara ta 1999 lokacin da mijinta Atiku Abubakar ya zama mataimakin shugaban kasar Nigeria.

Tayi amfani da damar ta wajen bayar da shawarwari don kawo karshen karuwanci da tilastawa yan mata dama sauran siffofin fataucin mutane. Da farko ita ce ta kafa Gidauniyar kawar da safarar kananan yara(WOTCLEF) sannan ta dauki nauyin wani kudiri mai zaman kansa don hukunci mai tsanani ga masu fataucin, ta kuma kafa hukumar hana fataucin mutane ta kasa, ta kuma gudanar da kwasa-kwasan ilimi na maraba da yan mata da gyara su da dawo dasu daga kasashe daban zuwa gida Najeriya.

Kyaututtuka

  • Annual Nigerian Women's Award (2002)
  • D'linga Award (2010)

Wallafe-Wallafe

Amina Titi Abubakar ta wallafa littattafai da dama wanda suka hada da:

  • Educating the Nigerian Child
  • Empower Law to Fight Child Slavery
  • Let Us Celebrate Humanity: A collected speeches on women's right and human trafficking

Kara dubawa

Manazarta

Tags:

Amina Titi Atiku Abubakar Kuruciya da IlimiAmina Titi Atiku Abubakar AikiAmina Titi Atiku Abubakar KyaututtukaAmina Titi Atiku Abubakar Wallafe-WallafeAmina Titi Atiku Abubakar Kara dubawaAmina Titi Atiku Abubakar ManazartaAmina Titi Atiku AbubakarGidauniyar Masu Fataucin Mata da Kawar da Aikin yi da YaraHukumar hana fataucin Bil-Adama ta Ƙasa

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

DageMusulunciPeugeot 807Gombe (jiha)GiginyaDandumeTarihin falasdinawaTufafiZaitunAbubakar Tafawa BalewaTantabaraInsakulofidiyaKabir Garba MarafaAdo BayeroDikko Umaru RaddaAnnabiAbba Kabir YusufAlhaji Ahmad AliyuMoroccoAbdullahi Baffa BichiPrabhasFarillai, Sunnoni da Mustahabban AlwallaHamza al-MustaphaEmilio SosaYolaIsah Ali Ibrahim PantamiUkraniyaTakaiNepalSankaran NonoJerin mawakan NajeriyaVietnamAlwali KazirGhanaKwara (jiha)Autism spectrumIsra'ilaPlateau (jiha)Wasan kwaikwayoAishwarya RaiJamhuriyar Dimokuraɗiyyar KwangoBOC MadakiKareSao Tome da PrinsipeFaustine FotsoMaliKhulafa'hur-RashidunIlimin taurari a duniyar Islama ta tsakiyar zamaniRabi'u Musa KwankwasoMata a cikin kasuwanciAnnabi YusufBasmalaGwanduFati WashaJerin SahabbaiBilal Ibn RabahaSoIbn HazmDauramaBilkisu ShemaCiwon Daji na Kai da WuyaNajeriyaZirin GazaHarshen uwa🡆 More