Al-Qur'ani (Larabci: القرآن al-Qur'an), ko kuma Alƙur'ani mai girma kamar yanda akasani, shine littafin da Allah ya Saukar a harshen Annabin Rahama, wato Larabci, kuma shine littafin da Allah ya rufe saukar da duk wani Littafi Mai tsarki a bayansa, (babu littafin da Allah zai sake saukarwa a bayansa) kamar yadda Allah ya saukar ga Annabawan da suka gabata, domin Annabi Muhammadu shine cika makin Annabawan Allah.
Alqur'ani mai girma | |
---|---|
Asali | |
Shekarar ƙirƙira | 631 |
Asalin suna | القرآن |
haɗawa a | Makkah da Madinah |
Characteristics | |
Genre (en) | religious literature (en) da religious text (en) |
Harshe | Ingantaccen larabci |
Kintato | |
Narrative location (en) | Yankin Larabawa |
Kallo
|
Wanda Allah ya saukar da ayoyinsa ga Annabin musulunci Annabi Muhammad (S A W). ta hannun mala'ika Jibrilu. A cikin aƙidar Musulunci, Ƙur'ani shi ne mafi muhimmanci kuma mafi girman mu'ujizar Annabi Muhammad (S.A.W), yana tabbatar da cewa Annabi Muhammad (S A W) Manzone na gaskiya.
Shari'ar Musulunci, wacce kuma ake kira sharia, ta dogara ne akan Ƙur'ani (Madogararsa na Farko), shine littafin da Musulmai suke karantawa, kuma suke aiki dashi, tare da hadisai Waɗanda suke sune maganar da fito daga harshen Annabi Muhammad. Musulmai suna karanta ayoyin kur'ani daban-daban a cikin addu'o'insu.
Lafiyayyan hankali da tsaftataccen tunani na ɗan Adam da ayyuka na yau da kullum sun tabbatar da cewa kur'ani ya bada cikakkiyar kulawa da kariya ta fuskar haƙƙin ɗan adam na duniya, da 'yancin ɗan adam.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Alqur'ani mai girma, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.