Aduwa tana daga cikin nau'in ita ce wato bishiyoyi sai dai kuma ita tana daga bishiyoyi masu 'ƴa'ƴa kuma ana amfani da 'ƴa' ƴanta ta fannoni daban-daban.
Ana tsotsan 'ƴa'ƴanta ana kuma anfani da man aduwa. An fi samun bishiyar aduwa a ƙasashen Afirka sai kuma wani ɓangare na yankin Asiya, a taƙaice an fi samun bishiyar aduwa a Sahara saboda haka ne ma turawa ke kiranta da Turanci da "Desert date" sai kuma akan same ta a wasu yankunan ƙasar indiya a yankin Rajastan (Rajasthan), Gujarat, Dekan (Deccan) da kuma Madiya Pradesh. Sai dai kuma ƙasar Sanegal ita ce ta fi kowace ƙasa bishiyar aduwa duba da bishiyar aduwa kusan ko'ina ana samunta a Senagal Tama fi sauran bishiyoyin yawa a ƙasar. Haka ana kiran ta da Turanci da (soap berry tree) ko kuma (thorn tree).
Aduwaa | |
---|---|
Conservation status | |
Least Concern (en) (IUCN 3.1) | |
Scientific classification | |
Kingdom | Plantae |
Order | Zygophyllales (en) |
Dangi | Zygophyllaceae (en) |
Genus | Balanites (en) |
jinsi | Balanites aegyptiaca Delile, 1813 |
Haka bishiyar aduwa tana tsawo sosai sai kuma 'ƴa'ƴanta kafin su bura ko kuma su nuna kore ne shar, idan kuma sun nuna sai su koma ruwan gwaiduwan kwai wato yalo (yellow). Sai kuma ɗan-ɗanonta tsami-tsami da ɗaci-ɗaci 'ƴa' ƴanta na da sauƙi wajen tsotsansu, haka aduwa tana da ƙwallo bayan an gama tsotsa ƙwallon ta yanada tauri sosai. Ganyen ƙanana ne bishiyar aduwa tana yin ganye sosai a yayin da ta kai shekaru biyar zuwa bakwai (5-7 years) haka tana fara ƴaƴa daga shekara goma zuwa sha biyar (10-15) sai kuma tana yin ƴaƴa masu yawa daga shekara ishirin zuwa ishirin da biyar (20-25).
Ƴaƴan aduwa suna da amfani sosai ga jikin Ɗan Adam ga wasu daga magungunan da takeyi:
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Aduwaa, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.