Kasar Libya tana daya daga cikin kasashen, dake Arewacin Afirika, kuma tanada iyaka da kasashe guda shida (6) su ne:-
Libya | |||||
---|---|---|---|---|---|
دولة ليبيا (ar) | |||||
| |||||
| |||||
| |||||
Take | Libya, Libya, Libya (en) | ||||
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Babban birni | Tripoli | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 6,678,567 (2018) | ||||
• Yawan mutane | 3.8 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Larabci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Bangare na | Arewacin Afirka | ||||
Yawan fili | 1,759,541 km² | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Bahar Rum | ||||
Wuri mafi tsayi | Bikku Bitti (en) (2,267 m) | ||||
Wuri mafi ƙasa | Sabkhat Ghuzayyil (en) (−47 m) | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Great Socialist People's Libyan Arab Jamahiriya (en) | ||||
15 ga Augusta, 1551: Tripoli Eyalet (en) 24 Disamba 1951: Masarautar Libya 1 Satumba 1969: Libyan Arab Republic (en) 2 ga Maris, 1977: Great Socialist People's Libyan Arab Jamahiriya (en) | |||||
Tsarin Siyasa | |||||
Tsarin gwamnati | jamhuriya | ||||
Gangar majalisa | House of Representatives (en) | ||||
• Chairman of the Presidential Council (en) | Mohamed al-Menfi (en) (15 ga Maris, 2021) | ||||
• Prime Minister of Libya (en) | Abdul Hamid Dbeibeh (5 ga Faburairu, 2021) | ||||
Ikonomi | |||||
Nominal GDP (en) | 39,798,423,941 $ (2021) | ||||
Kuɗi | Dinare na Libya | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | | ||||
Suna ta yanar gizo | .ly (en) | ||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | +218 | ||||
Lambar taimakon gaggawa | 190 (en) , 191 (en) da 193 (en) | ||||
Lambar ƙasa | LY |
Libya kasar larabawa ce kuma tana daga cikin kungiyar tarayyar Afirika kuma tana daya daga yan kungiyan kasashen larabawa da kungiyar kasashen musulunci, har zuwa yau ita 'yar kungiyar kasashen Arewacin Nahiyar Afirka ce, kuma yar kungiyar kasashen da suke da man fetur ne. Kasar Libya babbar kasa ce a wurin fadin Kasa amma sai dai mafi yawan kasar Sahara ce, Iyakar libya takai 1,759,540 km2 tanada babban iyaka da teku. Shugaban kasar daya shahara shine Muammar Gaddafi.
Libya da harshen misrawan da, wannan suna ya samu ne daga kabilar libo da suke zaune A jihohin da suke tsakanin Misra da Tunisiya.
dadin dadawa, akan kabilar libo kuma da akwai kabilu 'yan asalin Libya kaman Amazik da kabilar feneken. a karni na shida kafin haihuwar Annabi Isah daular kurtaja ta mamaye libya duk da karfinta Romawa sun kwace ta daga hannunsu, a karni na shida bayan haifuwar Annabi isah bizantinawa suka mamaye Libya. Kuma A karni na bakwai bayan haihuwar Annabi Isah sai larabawa suka shigo Libya
.
Libya ta samu ire-iren iko kamar haka:-
1 lokacin mulkin sarauta 1951 zuwa 1969
2 mulkin Moammar Gaddafi 1969 har yau Libya ta zama Jamhuriya tin 1977
Mutunen Libya sun kai adadin 6000,000 a sahile a arewacin kasar kabilolin Libya su ne, larabawa, barbarawa, tubawa karaglawa ( hadin turkawa da larabawa ), Buzawa da 'yan tsurarun ( hausawa da bare-bari ).
harshen larabci shi ne harshen kasar, larabcinsu yana da bambanci da sauran na kasashen larabawa kuma da akwai harsuna da yawa masu bambancin harshen ( Amazik, Buzanci tubanci da harshen Hausa ) shi ne harshen kasuwanci a birnin sabha da ke a kudancin kasar .
kuma Libya bata da shi'a samsam mabiya addinin yahudawa ( yahudawa ) yawancin su sun fita daga kasar bayan 1967 a yanzu saura 'yan tsirari a tirbule , Libya tana da 'yan tsirarun kyrke a tirbule da bangazi kuma suna da malamai kyrke daya yana Bangaze da zama
libya tanada jihohi talatin da biyu sune kamar haka:-
| ||
1 Ajdabiya | 17 Ghat | |
2 Al Butnan | 18 Ghadamis | |
3 Al Hizam Al Akhdar | 19 Gharyan | |
4 Al Jabal al Akhdar | 20 Murzuq | |
5 Al Jfara | 21 Mizdah | |
6 Al Jufrah | 22 Misratah | |
7 Al Kufrah | 23 Nalut | |
8 Al Marj | 24 Tajura Wa Al Nawahi AlArba' | |
9 Al Murgub | 25 Tarhuna Wa Msalata | |
10 An Nuqat al Khams | 26 Tarabulus (Tripoli) | |
11 Al Qubah | 27 Sabha | |
12 Al Wahat | 28 Surt | |
13 Az Zawiyah | 29 Sabratha Wa Surman | |
14 Benghazi | 30 Wadi Al Hayaa | |
15 Bani Walid | 31 Wadi Al Shatii | |
16 Darnah | 32 Yafran |
Ƙasashen Afirka |
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe |
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Libya, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.