Claude Monet

Claude Monet (14 Nuwamban shekarar 1840 zuwa 5 Disamban shekarar 1926) mai zane ne na kasar Faransa kuma wand aya kirkiro zanen impressionism, wanda Kuma ake gani a matsayin jigo na zanukan zamani, musamman yanda yake ƙoƙarin zanen yanayi a yanda ya fahimce shi.

A zamanin ayyukansa masu dogon tarihi, shine mafi shahara da kwarewa a salo zanen impressionism - wato falsafar zane ta hanyar fahimtar shi mai zanen ga wuri ko yanayi musamman zanen sarari (waje) da kuma yanayi ƙasa wato landscape. Kalmar "Impressionism" wato ra'ayin mai zane, ya samo asali ne daga zanensa mai suna Impression, Sunrise wanda aka gabatar a 1874 a wajen taron baje koli na Salon.

Claude Monet Claude Monet
Claude Monet
Rayuwa
Cikakken suna Oscar-Claude Monet
Haihuwa Faris, 14 Nuwamba, 1840
ƙasa Faransa
Mazauni Giverny (en) Fassara
Villa Saint-Louis (en) Fassara
Argenteuil (en) Fassara
Vétheuil (en) Fassara
Mutuwa Giverny (en) Fassara, 5 Disamba 1926
Makwanci Giverny Churchyard (en) Fassara
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (Ciwon huhun daji)
Ƴan uwa
Abokiyar zama Camille Doncieux (en) Fassara  (28 ga Yuni, 1870 -  5 Satumba 1879)
Alice Hoschedé (en) Fassara  (16 ga Yuli, 1892 -  19 Mayu 1911)
Yara
Ahali Léon Monet (en) Fassara
Karatu
Makaranta Beaux-Arts de Paris (en) Fassara : Painting
Harsuna Faransanci
Malamai Marc-Charles-Gabriel Gleyre (en) Fassara
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a painter (en) Fassara da mai zane-zanen hoto
Wurin aiki Faris, Argenteuil (en) Fassara, Vétheuil (en) Fassara, Poissy (en) Fassara, Giverny (en) Fassara, Honfleur (en) Fassara, Trouville (en) Fassara, Amsterdam, Oegstgeest (en) Fassara, Sassenheim (en) Fassara, The Hague (en) Fassara, Zaandam (en) Fassara da Landan
Muhimman ayyuka Zanen Ra'ayi, fitowar rana
Garden at Sainte-Adresse (en) Fassara
Houses of Parliament serie (en) Fassara
La Corniche near Monaco (en) Fassara
Water Lilies (en) Fassara
Rouen Cathedral Series (en) Fassara
Wanda ya ja hankalinsa Gustave Courbet (en) Fassara, Jean-François Millet (en) Fassara, Édouard Manet (en) Fassara, J. M. W. Turner (en) Fassara da Hokusai
Fafutuka Zanen Ra'ayi
Artistic movement landscape art (en) Fassara
still life (en) Fassara
Hoto (Portrait)
IMDb nm1217328
Claude Monet

Monet ya girma ne a garin Le Havre, Normandy, kuma ya fara sha'awar zanen waje tun daga ƙananun shekarunsa. Duk da cewa mahaifiyarsa Louise-Justine Aubrée Monet ta mara masa baya don cika burinsa na zama mai zane, mahifaisa kuwa wato Claude-Adolphe bai amince da hakan ba inda yake so ya zama dan kasuwa. Yana da kyakyawar alaka da mahaifiyarsa sai dai ta mutu ne a cikin watan Junairun shekarar 1857, a lokacin yana da shekaru goma sha shida a duniya, sannan aka turashi don yayi rayuwa a karkashin kulawar goggonsa attajira wacce bata taba haihuwa ba, Marie-Jeanne Lecadre. Daga nan ya zarce don yin karatu a jamiar Académie Suisse, kuma yayi karatu a karkashin shahararren masanin tarihin zane Charles Gleyre, kuma ya zamo abokin karatu ga Auguste Renoir. Ayyukansa na farko-farko sun hada da yanayin kasa, sassan teku, da zanen mutane wanda amma basu samu karbuwa ba da farko. Wani muhimmin mutum a rayuwar sana'arsa shine Eugène Boudin wanda ya koya masa salon zanen yanayi. Tun daga 1883, Monet ya cigaba da rayuwa a garin Giverny, wanda ke arewacin Faransa, inda ya siya gida da kuma fili kuma ya fara manyan ayyukan zanen filaye wanda suka hada da zanen korama na water-lily.

Burin Monet na ajiye kundin zanen yankunan Faransa ya kawo wani sabon salo na zane wanda ke daukar lokutan yini daban daban da kuma wucewar yanayi. Daga cikin wadannan zanuka na musamman da sukayi fice sun hada da zanen haystacks (1890–91), zanen Rouen Cathedral(1894), da kuma zanensa na Water lillies wanda ya kwashe tsawon shekaru ashiri yana yi.

Claude Monet
Claude Monet

Monet ya kara shahara da fice a cikin karni na 20, lokacin da ya zamo daya daga cikin muhimman masu zane na duniya kuma abun kwaikwayo ga sauran ƙungiyoyin masu zane da ke tasowa.

Tarihin Rayuwa

Haihuwarsa da yarintarsa

An haifi Claude Monet a ranar 14 ga watan Nuwamban shekarar 1840, a bene na biyar a gida mai lamba 45 da ke rue Laffitte, na garin 9th arrondissement of Paris. Shine ɗa na biyu ga mahaifansa Claude Adolphe Monet da kuma Louise Justine Aubrée Monet, dukkansu daga tsatso na biyu na mutanen Parisa. A ranar 20 ga watan Mayun shekarar 1841 ne aka masa baptiza a cocin Notre-Dame-de-Lorette, a matsayin Oscar-Claude, amma iyayensa na kiransa a saukake da Oscar. Duk da cewa anyi masa baptiza, Monet daga bisani ya koma mara addini.

Acikin shekara ta 1845, danginsa sun koma garin Le Havre da ke Normandie. Mahaifinsa, babban dan kasuwa yana so Monet ya shiga kasuwancin shigowa da kayayyaki don kasuwanci. Mahaifiyarsa kuwa ta kasance mawakiya ce, saboda haka ta goyo bayanshi a wajen cigaba da sana'ar zane.

A ranar 1 ga watan Afrilun shekarar 1851, ya shiga makarantar sakandare ta fasaha ta Le Havre. Ya kasance dalibi mai kwazo, bayan nuna kwarewarsa a zane, ya kasance yana yi wa abokansa da zane don samun kudi. Yayi darasinsa na farko a wajen Jacques-François Ochard, tsohon dalibin Jacques-Louis David. Acikin shekara ta Eugène Boudin, ya hadu da Eugène Boudin, wanda daga bisani ya karawa Monet karfin gwiwar fadada fasaharsa, kuma ya koya masa zanen waje (En plein air), kuma ya rike daukarsa don ziyarar wuraren zane. Monet ya dauki Boudin a matsayin malaminsa, "wanda ya gama masa komai" dangane da daukakar da ya samu daga baya.

Mahaifiyarsa ta rasu a cikin shekarar 1857. Ya cigaba da rayuwa da mahaifinsa inda daga baya goggonsa, Marie-Jeanne Lecadre; Lecadre ta cigaba da rike shi.

Paris da Aljeriya

Manazarta

Tags:

Claude Monet Tarihin RayuwaClaude Monet ManazartaClaude MonetZanen Ra'ayi, fitowar rana

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

HON YUSUF LIMANBobriskyJerin Sunayen Gwanonin Jihar SokotoChris Allen (1989)Francis (fafaroma)Sadiq Ango AbdullahiKabiru NakwangoLandanNejaLarry SangerSallar Idi BabbaAbdullahi MohammedSallar Matafiyi (Qasaru)Annabi IsahHadiza KabaraZazzauRafiu Adebayo IbrahimAmurkaAhmed MusaFati WashaBBC HausaShahoTAJBankDokar NajeriyaIbadanZakiBabban shafiTambarin NajeriyaDamisaShuwakaSani Musa DanjaFalasdinuJami'ar Al-AzharWizkidTaylor SwiftMusulunciKiwoMaleshiyaHarshen HausaAfrikaJerin gidajen rediyo a NajeriyaAfghanistanAhmadu BelloYakin Falasdinu na 1948KenyaAhmad S NuhuShugaban NijeriyaYadda Ake Turaren Wuta Na MusammanDJ ABSoyayyaOrder of the British EmpireJerin Gwamnonin Jahar SokotoAman Anand SinghWuhanNuhuƘungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta YammaKashiAfirka ta YammaZumunciDubai (masarauta)FezbukHadiza MuhammadArise PointShehu SaniIbrahim NiassJerin Sunayen 'yan majalisar wakilan Najeriya, 2019–2023Dahiru MohammedIbrahim TalbaShuaibu KuluMaganin gargajiyaTuwon masara🡆 More