Abinci: wani abu ne mai dauke da sinadarai na yayan itatuwa da tsirrai da dabbobi wadanda ake sarrafawa ta hanyar dafawa, domin ya gamsar ko ya gusar da yunwar ɗan Adam.
Misalin tsirrai da yayan itatuwa sune kamar: shinkafa, taliya, macaroni, doya, dankali wake (na Hausa Dana Turawa), masara, hatsi, alkama, dawa, alayyahu, rama, yakuwa, karkashi, kubewa, daudawa, kabewa, zogale, ayayo, tattase, tumatir, tarugu, da kuma kuka, tuwo, da sauransu.
abinci | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | disposable product (en) da physical substance (en) |
Bangare na | Q13538519 |
Amfani | eating (en) |
Kayan haɗi | food ingredient (en) |
Yana haddasa | food allergy (en) da satiety (en) |
Karatun ta | culinary art (en) da food science (en) |
Amfani wajen | organism (en) |
Unicode range (en) | U+2615,U+1F33D,U+1F345-1F37C,U+1F382 |
NCI Thesaurus ID (en) | C62695 |
Hannun riga da | non-food item (en) |
Sinadaran, abinci suna da yawa a fadin duniya inda dan Adam ke buƙatar su domin rayuwar shi.
Abinci shine duk wani abu da za'a ci don samun karfi da Lafiyan Jiki da kuma kuzari ga kwayoyin halitta na jikin dan Adam. Yana iya zama danye ko sarrafaffe ko tsararre, dabbobi na cin shi da baki don girma, ko samun lafiya ko jin dadi.
Abinci a duniya ya banbanta, domin bincike ya nuna cewa, mutane suna cin abinci daban-daban daga faɗin inda suka fito a duniya. Wani lokacin a kasa daya ko kuma jiha daya zaka samu mutane suna rayuwa amma kuma kalar abincinsu daban-daban ne.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Abinci, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.